KUSKUREN DA SUKE BATA SOYAYYA

 KUSKUREN DA MUKE ACIKIN SOYAYYA.

Ku nisanci yin abubuwan da zasu kaiku ga kun saba da juna a Soyayya, ku guji yin faɗa da masoyan ku. Idan har kuka so juna yanxu bai kamata anjima ku ƙi juna ba.

Lokacin da muke Soyayya, akwai wasu kuskure da muke wanda sukan iya jefa Soyayya cikin ruɗani ko takai ga rabuwa.

Kada mu manta idan an rabu ba sake dawowa, wasu mutanen kuma Ba'a iya maye gurbin su a rayuwa saboda muhimmancin su. Wasu sukan fahimci kuskuren su, amma wasu basa ganewa.

Ga wasu Kuskure da Muke acikin Soyayya, waɗanda ba daidai bane, hasalima sukan iya jawo rabuwar Soyayya.

1. Juya Masoyi Ta Hanyar Da baya so.

 Yawancin mu muna da matsala ta son juya wanda muke so da ƙauna. Hakan takan janyo muna neman sani a game da duk wani motsi na abunda muke so. Yayi da muka tsinci abunda bama so, sai muyi kokarin hanawa ta hanyar da bai dace ba.

Mu Kula da wannan: Zaka so wani ko wata su faɗa maka abunda zaka yi koda yaushe?? Kai ba babanta ko mamanta ba, idan har Babbane, to ɗaukeshi da muhimmanci kuma Girmamawa ya shigo. 

2. Kada Ka Raina Wanda Kake So.

Mutane suna raina wanda yake son su ba wai ko basa son su bane, sai dan suna tsammanin wanda suke rainawan bazai guje su ba, so sai su raina wanda suke Soyayya dashi ko da ita, har ɗaya ya gaji ya fara neman a rabu. Idan kuna Soyayya ta gaskiya mai kyau kada ku sako raina ko wasa yayi yawa.

3. Yawan Faɗa akan komai.

Duk irin Abunda Masoyi zai yiwa masoyi na rashin jin daɗi kada ku juya shi ya dawo faɗa. Kuyi ƙokarin kaucewa irin wannan. Sannan Hakuri yana da riba a Soyayya sosai Na Baku wannan #Laƙanin ku gwada shi.

4. Yabon Tsohon Saurayi Ko Tsohuwar Budurwa akan Wanda ake tare dashi ko ita.

Kishi wani abu ne dake saurin tayar da hankalin mutane, wajen sanya su fishi mai tsanani ko ma yin faɗa. Dan haka a kiyaye Yabon Ex A Kusa da New Ina Fatan Kun gane. 

Abubuwan da suke bata soyayyaKaranta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-BA'A-JUREWA-SOYAYYA

5. Tsammanin Ramako

Kada Kayi Soyayya dan a rama maka, domin wataƙila wacce kake so ko take sonka bata iya Soyayya ba, kada ka ɗauka idan kai mata kalaman Soyayya guda Goma zata dawo maka da biyar. Wasu sai an koya musu yadda ake Soyayyar ma sannan a koya musu yadda ake rubuta kalaman Soyayyar.

Sannan yana da kyau ku zauna ku fahimci juna ku faɗawa junan ku yadda kuke son kuyi Soyayya, me kake so ana yimaka, itama ta faɗi abubuwan da take so, sai ku gyara Soyayyar ku ba wanda ya sani.

6. Girman Kai

Wasu mutanen suna da girman kai wajen bayyana Soyayyar su, daga ƙarshe sai rasa wanda suke son da gaske. Idan kana son wata, ko kina son Wani, Tell her or him. Idan baka faɗa ba, zakai dana sani walau mace ko namiji. Waɗannan kalmomi Guda ukun "I Love you" suna da matuƙar amfani acikin Soyayya amma ba kowa ke ganewa ba.

DuniyarLove

Post a Comment

Previous Post Next Post