YADDA SOYAYYA YA RABU KASHI BIYAR

YADDA SOYAYYA YA RABU KASHI BIYAR

Soyayya kamar Jin yunwa ne da Ƙishirwa, da bacci, dole ne ɗan adam yayi rayuwa dasu. An ɗau tsawon lokaci ana wajen neman yadda Za'a fahimci Soyayya wajen rubutu akan SO, cikin waƙa, yabo ko a fina-finai, Amma har yanxu mun kasa fahimtar Soyayya saboda yana chanja ma'ana ako wace rana. Duk da haka munyi ƙoƙarin kawo wasu daga cikin Ire-Iren Soyayya: 

1. Liking

Wannan wani Nau'i ne na Soyayya wanda shine yafi yawo musamman ga abokantaka. Kana son mutum ne kawai amma badan ka aureshi ba, sai dan wani abu da ka gani ajikin shi kana so. Amma babu wani abu mai muhimmanci bayan haka.

2. Infatuation

Wannan Nau'in Soyayya zalla tare da Sadaukarwa, babu wasa ko jan ra'ayi.

Irin wannan son mutane ke ji idan suka ga wanda suke so a farkon fari, wanda ake kira Da Yaren English (Crush or Love at First sight). Wannan Soyayyar itace wasu ke kira Soyayyar Gaskiya. Babu komai acikin ta face zallar aminci da amana tare da wasanni na ƙara shauƙi da ƙaunar juna, har ma takan iya juyewa zuwa Ga Yin Aure.

 

Types of loveKaranta: YADDA AKE ZUWA WA AMARYA DAREN FARKO

3. Empty love

Soyayyar da take zaunar da mata da miji kenan, amma badan suna son juna kamar da ba, sai dan suna da ƴaƴa. Suna zaune ne kawai dan ƴaƴan dake tsakanin su, ko wani yarjejeniya da sukai wa junan su. Irin wannan Soyayyar dama acikin aure ake samunta.

 

4. Romantic love

Wannar Nau'in Soyayyar tana da ƙarfi sosai harma da shauki tare da mararin juna, amma babu sadaukarwa acikinta. Kawai kuna Soyayya ne dan matsayin ɗaya daga cikin ku, maybe ƙuɗi, mulki ko wani abu mai kama da haka, idan Ba'a kula dakyau ba akan iya faɗawa irin wannan Soyayya. Irin wannan Nau'in son yana faruwa ga abokan da suka jima suna tare, kuma sun shaƙu, kamar dai Ace BESTY.😂


5. Fatuous love

Wannan Nau'in Soyayya ana ce masa maza-maza, wato Soyayya ce da ake fara ta cikin ƙanƙanin lokaci daga wannan Stage ɗin zuwa wani. Sannan Takan saka yin aure acikin lokaci kaɗan ba tare da tayi tsawo ba.


Wasu takan iya ɗaukarsu kwanaki ko watanni ko shekaru, ya danganci irin ƙarfin alaƙar dake tsakani ce.

DuniyarLove❤🙋🏻‍♂

Post a Comment

Previous Post Next Post