YADDA ZAKA GANE ADADIN SOYAYYAR DA MACE TAKE MAKA.

 YADDA ZAKA GANE ADADIN SOYAYYAR DA MACE TAKE MAKA.

Ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci a rayuwar mutane shine samun Soyayyar gaskiya. Kuma akan iya sadaukar da komai domin aga an mallaki Soyayyar gaskiya. Wasu matan da mazan na cewa suna shan wahala kafun su gane wanda suke so yana son su.

Waɗannan wasu hanyoyi ne masu sauƙin bi domin gane wacce kake so tana son ka yadda kake so. Ko wace mace idan tana sonka, to zatai ƙorafin waɗannan abubuwan da zan zayyano da zarar ka fara nuna su.

Acikin wannan Rubutun Zan Suburbuɗo Hanyoyi Huɗu (4) dw zaka Gano kuma ka tabbatar Mace na sonka.

1. Ka daina kiran ta sosai.

Wannan yana da wahala wani ya gane yadda mace take son shi. Idan ka daina kiranta, idan tana sonka sosai, to zata shiga damuwa kuma ta kiraka da kanta.

Damuwar dama ka gane shin ta damu dakai ne ko bata damu ba, daganan kasan inda Soyayyar ka ta dosa.

Karanta: YADDA NAMIJI ZAI MALLAKE ZUCIYAR MACE CIKIN SAUƘI

2. Ka Faɗa Mata Ka Samu Karayar Anjihu.

Duk Macen da take sonka tsakani da Allah to zata zauna tare dakai komin talaucin ka, Hali mai kyau ko maras kyau. Idan har ta cigaba da zama dakai to lallai tana Ƙaunar ka. Idan kuma ta juya maka baya ta nuna halin rashin Nagartar ka ya dameta, to sai ka nemi wata hanyar domin wannar akwai GARGADA.

Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DAKE CUTAR DA MUTUM KULLUM

3. Kar Kana Maida mata Message Akan Lokaci.

Wannan ma yana aiki. Idan ka ɗan ja baya da maida mata Message akan lokaci, zata fara maka ƙorafi ranta zaina baci. Sannan zatayi komai domin ta tabbatar ka dawo kanta. Wata ma saita kiraka na musamman domin ta tambayeka Shin Baka ga Message ɗina bane?. Kana ganin Akasin Haka, sai kasan irin takun da zakayi.

Karanta: ABUBUWAN-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA MASU AMFANI

4. Ka Rage Zuwa Hira.

Idan Kana yawan zuwa wurinta hira, to ka rage ka ɗan ɗauke ƙafa. Idan tana sonka, bazata ji wani ɗarɗar ɗin Tambayarka dalili ba. Wata ma sai ta nuna damuwa ko fishi akan hakan. Alamu ne dake nuna tana son ka.

Post a Comment

Previous Post Next Post