ABUBUWAN DA YAKAMATA KA SANI AKAN SOYAYYA.

 ABUBUWAN DA YAKAMATA KA SANI AKAN SOYAYYA.


KALAMAN HIKIMA

Gina Soyayya mai kyau kuma mai tsafta yana zuwa ne daga yin aiki tukuru na Masoyan dakuma jajircewa da suka yi. Ga wasu abubuwa da yakamata ku sani.

1. Bazaka Taba sa wata ta soka ba wai dan kana mata abubuwan da takeso batare da tana so ba. Da zarar ka kasa son kanka, to bazaka taba iya son wata ba. Wannan shine gaskiya. Zaka iya son wani ko wata ne idan ka fara son kanka.


2. Faɗawa Soyayya Abune mai sauƙi, Kasancewa acikin Soyayya ƙalubale ne babba. Sake jiki yana da walaha, amma Neman hanyar cigaba yafi wahala. Dole ne ka samu wacce take sonka, wacce bata tinanin ka saidai Tana ganin ka a zuciyarta. Wacce bazata wahalar dakai ba.

Karanta: ABUBUWAN DA MATA SUKA TSANA


3. Koda yaushe akwai abunda kowa keso a tattare da ita, kuma shine zabin su musamman wajen ÆŠaukar hankali, har da Soyayya

4. Kiyaye Soyayya akwai wahala. Wannan shiyasa wasu masoyan daga ƙarshe rabuwa ta shiga tsakanin su koda kuwa suna Son junan su bazasu iya gudanar da ita yadda ya kamata ba.


Love images

5. A ko wace Soyayya, koda yaushe kana tinanin me zaka iya dan ka burge batare da kaima anyi maka ba. Kada ka sake ka sanya farin cikin ka akan abunda Budurwar ka zata maka dan kayi mata abun kirki.


6. Kasancewa masoyi Yana nufin duk abunda kayi, to ya zamo yayi daidai da abunda wacce kake so take so. Yawancin masoya sukan rabu saboda Soyayyar ta ƙare kuma sune suka ƙarar da ita. Sun rabu ne kuma saboda ɗaya daga cikin su ya daina baiwa ɗaya Isheshshen Lokaci ko rashin kulawa, tattauna matsaloli ko yawan zargi, dakuma rashin baiwa juna haƙƙi.


7. Yawan Murmushi wa juna wata alama ce dake nuna farin ciki a fuskar masoya. Amma abunda murmushin ke nufi wannan sai an tambayi Zuciya, shin na farin ciki ne kona baƙin ciki ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post