MATA DA MAZAN DA SUKA CANCANCI AURE.

 MATA DA MAZAN DA YAKAMATA MU AURA

Akwai wasu Mata da Maza da yakamata mu aura amma wasu basu sani ba sai an buɗe musu idanu ko an wayar dasu.

Anan Mun kawo muku su amma a taƙaice:


Duk Macen da Bata da Addini, Ba Cancanci A Aureta Ba!!!

Duk Macen da ta ɗauki duniya wajen zama.

Duk Macen data Sanyawa Kanta Girman Head.

Duk Macen da bata da Ilimin Addini.

Duk Macen Da Bata da Wayewa Game addinin ta.

Duk Macen Da Bata Iya Girki Ba.

Duk Macen da Bata Iya Ƙasƙantar da Kanta ga Namiji Ba.

Duk Macen Da Bata Ta Sanya Kwaɗayi a Ranta.

Duk Macen da Bata Iya Zama da Mutane Ba (Mu'amala).

Wannar Macen ta Cire kanta daga Layin Wanda Suka Kai Aure, Domin har yanxu Ba matar aure bace. 

Ita Mace Al'umma ce Idan batayi Kyau ba, Ƴanƴan da zata haifa Zasu lalace idan ba taimkon Allah. 

Kada kisa a ranki cewa Mai Kuɗi shine miji na gari, hakan kuskure ne. Miji na gari shine wanda yasan haƙƙoƙin Matar shi, kuma yana bata Wannan Haƙƙoƙin Bai Tauye Koda Ɗaya ba.

Ba ruwanki da Mai Ƙuɗi ko Talaka, Allah Ne yake yadda yaso, ga wanda yaso.

Matan tik tok


Duk Namijin Da Baida Addini.

Duk Namijin Da Baida Sana'a.

Duk Namijin Da ake baiwa Ƙuɗin Sabulu a gida.

Duk Namijin Da Baya Iya Ɗaukar Nauyin Kanshi.

Duk Namijin Da Yake da Mugun Halaye.

Duk Namijin Da Baida Abokan Kirki.


Wannan Namijin Bai Kai Aure Ba, Aure Bana irin Ku Bane.

Kada Mace Ta Kuskura Ta Auri Mijin da Bayada Sana'a Zata sha Wahala Duk Haƙurin ta.

Munsan Allah ne keyi, amma Allah Bai ce ka kwanta a gida Kuɗi yaxo ya sameka ba. Dole saika fita ka nema. Waƴanda suka fika Daraja A Musulunci Sune Sahabbai, To Suma Ƴan Kasuwa ne.

Wannan Shawari Ne Kyauta Daga Qauna Site

Post a Comment

Previous Post Next Post