YADDA HARSHEN MACE KEDA QARFI

ƘARFIN HARSHEN MACE!!!


Yaya Girma da kuma ƙarfi na Harshen mace yace? 

Idan aka ce Harshe ko Harce duk abu ɗaya suke Nufi, Shine Furcin baki. Indai Zaka buɗe baki Kayi Magana To harshe ne Silar wannan Maganar.

Kamar yadda muka sani Mace tana da matuƙar daraja acikin wannan zamanin kuma mata suna bada Gudummawa sosai Wajen gyaruwar Zamani ko Akasin Haka.

Yadda Ƙarfin Harahen mace yake:

1. Babban ƙarfin Mace Shine Kalaman ta, Koda yake maza sun fi mata Ƙarfi a zahiri, amma mace takan iya Danƙwafar da Namiji Ta Maidashi ba komai ba da Ƙarfin Harshen ta.

Karanta: RABE-RABEN-MATA-SOYAYYAR-ZAMANI

2. Kalaman Mace zai iya Ƙarfafa namiji kuma ya zamar masa kamar wata Katanga, ko ya hana shi tabuka komai a rayuwar shi. Iya Adadin Soyayyar da yake wa mace, iya adadin Ƙarfin ta akan shi.

3. Harshen Mace zai iya tarwatsa ƴaƴan ta data haifa ta fuskar tsanantawa ko Sassauta kalaman ta. Kalaman mace kan iya ƙarfafa ƴaƴanta wajen samun gobe me kyau, Imani da Soyayya. Yadda yara zasu ke tinawa da yarintar su ya ta'allaƙa ne da Yadda mahaifiyar su ke Musu Magana, Hira Umarni da Tarbiya.

Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA

4. Harshen Mace yakan zama wani zabin da mazaje da yawa ke so wajen Son kasancewa da mace. Irin waɗannan matan sukan zama ababen Sha'awa. If she is single, she misleads men; if she is married, she makes her husband insecure as he wonders why she speaks to other men with a sexual undertone.

5. Harshen Mace Kan iya Chanzawa abokai hanya, Tinani da Aƙida da iya kalaman ta. Harshen mace kuma yakan saka abokai zama da ita saboda Iya Faranta musu, Yadda take kulawa da Kowa.

Karanta: DOKOKI 40 DAYA KAMATA DUK WANI NAMIJI YA SANI

6. Harshen Mace kan iya zama Na'ura ta tsegumi, kuma ya sanyata Zama kusa da Abokai masu tsegumi, A Hankali Su Tarwatsa kansu, Auren su, Kyawawan Aikin su, Zaman lafiyar su, da duk wasu mutane dake Kusa dasu. Da Iya Harshe

7. Harshen Mace Zai iya saka Mijin ta Yana ƙin dawowa gida da Wuri, ya dinga dawowa very late saboda ya gujewa Maganganun ta, kuma bawai wasu mata zai bi ba. Haka Harshen Mace Kan iya Saka Namiji Dawowa gida akan lokaci saboda yanason zama da ita, kuma zai iya wuni yana waya da Ita batare da ya gaji ba, saboda Harshen Ta.

Karanta: DABARU 15 DA MAZA KE AMFANI DASU

8. Macen da Take abubuwa cikin fishi tare da ganganci da Harshen ta, zatana fitarwa da Faɗin Maganganun da basu kamata ba. Macen data Kiyaye Harshen ta tana kula da Faɗin bakin ta, koda Tana cikin bacin rai Tana taka tsan-tsan da Harshen ta.


Karanta: ABUBUWAN-DA-MATA-SUKA-TSANA


9. Harshen Mace Zai iya zama Wani Makami da zai iya Tarwatsa Namiji da Kalamai Zafafa Kamar Su" Kai Ba Ajina Bane", "Kai Talaka Ne", "Ka Ta6ani Ka Gani". Harshen Mace Yakan Iya Zama Peace Maker, Mafi daɗin Kwantar da Hankali wajen da ake Rikici, Hatta Wutar data tashi yakan iya kashewa kafun tayi 6arna, Fahimtar da Mijin ta ko Saurayin ta dakuma Nuna Masa Yabo.

10. Harshen Mace Zai Iya Tarwatsawa ko Gina Gidan Da Take Ciki. Da Sautin Muryarta zata saka kowa Cikin halin da Taso.

Karanta: ILLOLIN CIN NAMA DA YAWA, MUSAMMAM JAN NAMA

11. Kalaman Mace Zasu Iya Dakatar da Cigaban ta, Mafarkin ta da Addu'oi nta. Kuma tayi amfani da wannan Harshen wajen gyra, bada Umarni, Kyautatawa Mijin Ta da Saita Rayuwar Ƴaƴanta, da Al'umma Duka.

Akwai Ƙarfi a Harshen Mace!!!

Post a Comment

Previous Post Next Post