ILLOLIN SHAN RUWA MAI SANYI

ILLOLIN SHAN RUWAN SANYI ICE WATER

Tabbas ruwa shine jigon rayuwa, Saboda shi jiki yake sarrafawa domin aikin yau da kullum. Amma yana da illa idan ya Zama ƙanƙara ko yazama me sanyi da yawa (Ice water).

A jikin dan adam akwai wani sinadari da ake kira (mucus) kamar majina take ana samun ta a sassan jiki kamar ciki da maƙogwaro. To shi ruwa me ƙanƙara ko me matuƙar sanyi idan ka sha shi zai haifar da wannan sinadari na mucus dayawa a jiki. Wanda yawan sa a jiki kan haifar ma da garkuwar jiki naƙasa. Wanda hakan kansa jiki yayi saurin kamuwa da cuta, sannan kamar masu zazzabi ba'aso ana zuba musu ruwan sanyi saboda yana haifar masu da (chilly) ma'ana matuƙar jin sanyi, Ana so a zuba musu ruwa me dan sanyi ne.

Ruwa me matuƙar sanyi ko me ƙanƙara na haifar da matsala aciki da hanyar narka abinci wato digestive systm.

Kadan daga cikin illolin ruwa mai matuƙar sanyi ko ƙanƙara: 

1. Yawan shansa na haddasa mura:  Itakuma Mura Tana Kawo Yawan Tari, Yawan Fitar da Majina, Yawan Atishawa, Toshewar Maƙogwaro, Toshewar Hanci, da Cutar Nimonia.

Ice Water

Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA


2. Jin sanyi: Yawan Yin Zazzabi, Kuma sanyi zaina takuramaka komai kaɗan ɗinshi zakaji ya takura maka.

3. Zafin Maƙogwaro ko ciwonsa: Ƙuraje zasu fito maka a Maƙogwaro Su Hanaka Cin komai ko sha, idan ka daure zaka sha ko zaka ci zasu na maka zafi.

4. Me yawan shan Ruwan Sanyi zakaji Idan yana numfashi zakaji yana ƙara kikir-kikir haka daƙyar zata na fita.

5. Shan Ruwan sanyi yana kashe Sha'awa Ga mace da Namiji. Sannan yana kawo Ƙarancin Ruwan Mani.

Karanta: YADDA-AKE-CHATTING-DA-BUDURWA

Da sauran matsaloli a jikin mutum wanda bamu kawo ba. da fatan zaku kiyaye shansa. koda zaka sha to kasha wanda baida sanyi sosai.

Sannan kuma shan ƙanƙara irin wanda ake sayowa a buhu ana sayarwa a layi ko kasuwa, itama shanta na da illa dan bata da tsafta, hasali ma ita badan ta narke asha suka yi taba, sun yita ne dan masu preserving (adana) kayan da zai iya lalacewa kamar kaji, kifi, ko acikin kayan shaye-shaye kamar pure water, zobo ko lemo. Amma a tabbata an wanke ita Ƙanƙarar kafin a fasa akai.

KARANTA: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA

Sannan a kiyaye koda ta narke abun yayi sanyi to kafin asha a wanketa. Wato kamar zo6on, ko pure water wato kada asha ruwan Ƙanƙarar

Ko Ana sayan Ƙanƙarar pure water tafi tsafta da inganci.

Idan ba'ayi sa'a ba saika ga ta haddasa cututtuka kamar, Amai da gudawa dasauran su. dan haka in za ayi amfani da ita din asami mai tsafta. Sannan akuma sirkata sosai ta yadda sanyin bazai yi illaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post