ABUBUWAN DA MAZA KE SO A JIKIN MATAN DA SUKE SO

 ABUBUWA 7 DA MAZA KE SO A JIKIN MATA A BOYE.


Idan Namiji ya faɗa Soyayya da mace, akwai wasu abubuwa da yawa ƙanana game da ita da suke saka shi Murmushi bawai kawai a fuskar shi ba, har Zuciyar shi.

So, Menene waɗannan abubuwan da Namiji yake so a game dake amma bazai faɗa miki ba?

1. Duk lokacin da namiji ya tina dake yana yin Murmushi indai yana sonki. Koda yana aiki ne, koda Yana ciki Damuwa ne, daya tina ki sai yaji ya wuce. Idan har Namiji na son mace kuma yayi Sa'ar Mace, koda basa tare Zaina farin ciki idan ya tina irin Halayyar da take nuna mishi

2. YANA SON YAGA YA SAKA KI MURMUSHI

Kin taba kula cewa idan na miji yaga kinyi Murmushi shima yana yi? Idan namiji mai abun dariya ne yakan yi iya bakin ƙoƙarin shi domin yaga kinyi Murmushi, dariya, dakuma Baki lokacin shi. Kuma yana son ace shine yasa kikai wannan farin cikin.


Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA


3. YANA SON KASANCEWA A KUSA DAKE. 

Idan namiji na son ki, zakiga koda a cikin mutane ne zaina son zama kusa dake, yana son koda yaushe ki kasance tare dashi. Yana gina shauƙi sosai kasancewa kusa da wanda kake so.

4. YANA SO KIYI MURMUSHI BAYAN YA SUNBACE KI. 

Sunbata Nada tasiri Sosai a Soyayya, kuma wata hanya ce da take da saurin isar da saƙon Zuciya zuwa ga zuciya.




Karanta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-BA'A-JUREWA-SOYAYYA


5. YANA SON YANA KAMAKI KINA KALLON SHI.

Kowa yana son ana sonshi, ana Ririta shi. Yaji cewa shima fa akwai wacce take ji dashi. Idan kina yawan kallon Namiji zaisa yaji yana ƙara ƙaunar ki sosai, sannan zaina yawan yi miki abunda kike so batare da kin tambaya ba.

Idan muna tare da mace wacce take matuƙar so ta zauna damu wacce take mana Soyayya irin wacce muke mata, wacce take bamu farin ciki, yarda, aminci, da Soyayya kamar yadda muke mata, babu abunda zaka nema ga mace kamar Haka a duniya

6. YANA SON YAGA KINA YIN WANI ABUN DARIYA DA BAKI SAN KINA YI BA.

Misali: kina Murmushi har dimple naki ya bayyana, ko kina Rufe fuska idan ya baki dariya, yawan jin kunya, ko wata magana da kike acikin zance da yake son Yana jin haka. 

Wasu mazan ma har So Suke suna Tsokanan Mace Idan suna son Tana yi musu irin wannan Abunda dan kawai suji daɗi.


Karanta:HALAYEN-MATA-TA-GARI


7. YANA SON KINA GIRMAMA SHAWARIN SHI.

Idan Namiji ya fahimci cewa kina Girmama Shawarin shi idan ya baki yana ƙara mishi shauƙin sonki Sosai. Domin ɗaya daga cikin daɗin zama shine Girmama ƙudurin juna, musamman ta fuskar Halayya.

Sannan Kina neman Shawarin shi, kina yawan Tambayar shi menene tinanin shi akan abu kaza. Idan namiji yana yawan baki shawari shima zaina Tambayar ki shawari, kuma duk irin wacce kika bashi zai ɗauketa da muhimmanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post