YADDA AKE GANE SAMARI MA'YAUDARA

 YADDA AKE GANE SIFFOFIN SAMARI MA'YAUDARA


Ƴar uwa kisani samari mayaudara sunfi samarin kirki shiga rai, sun fisu iya nuna so da ƙauna a gareki. Sukan kwantar da kai agareki komai wulaƙanci, gasu da azababben naci tun kina ƙin kula su har sai sunjawo hankalinki. Hakan Tasa Gane Saurayi Mayaudari Abune Maiwuya Domin Abune Dake Zuciya Sai Dai In Kinbi Wasu Matakai.

DABARUN DA SAMARI MAYAUDARA SUKEBI DAN YAUDARAR YAN MATA.

1. Dafarko sukan yi taget ɗin budurwar da suke so su yaudara imma dan kyanta, ko halittarta ko ƙimarta kowani dalili nasu kodan fasiƙanci.

2. Su Kanyi nazari akan halayenta kamar aƙidarta me tafiso wato idan ita ustaziya ce sukan yi shigar ustazai suzo gunta insungadama sukan riƙo littafi na ustazai su zo gunki kamar salasa usulu, kitabul tauhid.

Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

Idan ke sayyadace sukanyo miki shigar ya sayyadi suzo miki hira in sun ga dama sai su riƙo diwani ko wani dan littafin na ƙasida.

Idan ke me yawan karatun soyayyace sai su zomiki da littafan soyayya sabin shigowa ko cigaba wani littafi shahararre, yana riƙe a hanunsu.

Idan ke ma abociyar son holewace haka zai yo miki shiga ta yan holewa.

Inke abar tausayi ce zaizo da sunan zai taimakeki har makaranta ma zai saki

Zaina bin ra ayinki, bai son saba miki gasu da daɗin baki sukanyi miki kuka ko su durƙusa miki ƙasa suna baki haƙuri sukan faɗa miki kalaman kwantar da hankali da rantsuwa wadda saurayi na kirki bazai iya faɗa miki ba.

WANNAN SUFFOFIN NASAMA SIFFACE TA SAMARI MA YAUDARA AMMA SUNFI YIN AMFANI DASU WAJEN ƘANANAN ƳAN MATA KAMAR YAN SHEKARA 18 ZUWA QASA. 

Sakamakon ƴan mata a wannan lokacin suna da naƙasu sosai a tunani a wannan lokacin soyayya kawai suka sani sukan bujirewa kowa akan soyayya koda iyayen sune.


Karanta: ABUBUWAN-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA

3. Idan Samari Zasu Yaudari Manyan Yan Mata Sukan Yaudare Sune Da Kuɗi Ko Abubuwan Duniya Sakamakon Awannan Lokacin Su Manyan Mata Daka Shekara 20 Zuwa Sama Su Matsalar Su Mota, Kudi Da yawa Dasauran Su.

4. Abubuwan Rayuwa Kamar Ara Mata Mota, Yimata Qaryar Za Asaya Mata Mota Ko Wasu Abubuwan Har Sai Ta Saki Jiki Sannan A Yaudare Ta Agudu.

5. Wasu Mayaudaran Samari Sukan Kai Kayan Tambaya, Ko Ma Kuɗin Aure Ko Su Tura Iyayen Su. Amma Daganan Basa Sake Aiko Komai Sai Suyi ta soyayya da budurwa har sai sun yaudareta.

6. Wasu mayaudaran samarin sukan yaudareki da haɗin bakin abokan sa tahanyar shirayamiki makirci. Kamar Samiki Kwaya A Lemo Da Sauran Su.



Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE


DALILIN DA YASA SAMARI SUKE YIN YAUDARA.

1. Ɗaukar fansa. Wato watace ta yaudare su sai su kasa yin haƙuri sai suje su yaudari wata.

2. Rashin tsoran Allah swt na haƙiƙa.

3. Son suyi fasiƙanci da budurwa.

4. Samun budurwar da za ana zuwa fati dasauran guraren holewa da ita.

Karanta:SHAWARI GOMA GA MASOYA

YADDA ZAKIYI MAGANIN MAYAUDARI.

1. Kada kitaba yadda ki zurfafa a Son saurayi ko wayeshi kuma kome yakawo gidan ku.

2. Kizama mai yawaita addu'a da neman kariya daga sharrin samari mayaudara.

3. Kada ki kuskura kiyi yaudara.

4. Idan saurayi yazo kafin ki amshi soyayyarsa kibashi aƙalla kwana 2 ko sati 1, kafinnan kije kiyi istikhara akan sa, insha Allah inbana gari bane bazai dawoba Allah zai wargatsa nufinsa akanki.

5. Ki yawaita shigo da iyayenki dana sa cikin al'amuranku na soyayya.

6. Kada dan yakawo miki kudin aure kisaki jiki dashi.

Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA

7. Dazarar kinga janci atare dashi KI CANCAREMASA KARKIYIMASA DAWASA SAURAYI MATASHI MASIFA NE ACIKIN MINTI GOMA ZASU ZUBA MIKI DAFIN DA ZAI SHAFE TARIHIN RAYUWARKI, YA TOZARTA KI DA DANGINKI DUKA, ya Ƙasƙantar dake, yabata tarihin zuri'arki shikuma yayinasa gu.

Danhaka Ƴar Uwa Dakin Fuskanci Saurayi Mayaudarine To Kici Ubansa Ki Taramasa Jama'a Dan Kar Yasake Zuwa Unguwarku. Inyaje Gaba Yafaɗawa Abokansa Mayaudara Yadda Kika Yi Masa Zasu Na Shayin Unguwarku.

Samari mayaudara abokan junane sukan taimakawa junansu da labarai da abubuwa. su kanyi musanyen unguwa ɗan wannan unguwar ya bawa ɗan wancan unguwar sirrin unguwar.

Kaso 75 na samari mayaudara sunayine dan su lalataki imma dan su kwanta dake kodan suna wasa dake.

Post a Comment

Previous Post Next Post