YADDA AKE ZAMA DA MIJI ME SAURIN FUSHI

 YADDA AKE ZAMAN AURE DA NAMIJI ME SAURIN FUSHI.


Shi Fushi Ɗabi'a ce ta Ɗan adam, kowane mutum yana fushi, akwai sinadaran fushi acikin ƙwaƙwalai da suke a tare wanda ɗan adam ke gadonsu daga iyayen sa idan kana da sinadaran da yawa sai kazama me saurin fushi kenan.

Idan Mace Ta Auri Namiji Me Saurin Fushi To Tana Cikin Matsala Idan Bata bi A Hankali Ba Watarana Abu Kadan Zai iya Sawa Ya Mata Duka Ya Farfasa Mata Jiki Harda Karaya Haƙori Wani Kan Iya Karyawa Mace Qafa Ma.

Ƴar Uwa Idan kina Da Namiji Me Yawan Fushi To Ana So Kizama Me Lura Sosai Da Waɗannan Abubuwa.


- Me yake saurin sa shi fushi da tunzura

- Me yake saurin sauƙo dashi in yayi fushin ?


Karanta: AMFANIN AUREN BAZAWARA KO WACCE TA GIRMEKA


- Wani namijin bayason yawan surutu in yana jin yunwa, ko in yadawo daga gun aiki.

- Wani namijin yakan ji saurin fushi in bashi da Kuɗi ko yaje sana'arsa bai samo komaiba.

- Wani kuma yafi fushi da 6ata rai in yasami Kuɗi ko ya ɗauki albashi duk dan karki dameshi da kin matsa kuwa Za'a 6ata.

- Wani idan aka 6ata masa rai a waje koda a musune sai ya dawo gida da fushi dazarar kin tsokanoshi kaɗan sai ki taka sawun barawo yayi ta miki masifa inba kiyi wasa bama yayi miki duka.

- Wani baya so yanai miki magana kema kina masa magana sai yayi fushi ya harzuƙa zaiga kin ma raina shi yana magana kina magana yafiso in ya faɗa kiyi shuru har sai ya gama.

- Wani Kuma Hakan Yatsana Yafiso Yana Faɗa Kina Faɗa Da Kinyi Shiru Sai Ya ɗauka Kin Raina Shine.


Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWAREWA-SOYAYYA


- Wani kuma baya son gatse ko zolaya ko yawan wasa nan-da-nan sai ya hau fushi.

Dan haka ke zaki karanci halin mijinki kisan yadda yake dakuma hanyoyin da zakina mu amalantarsa.

* Sannan Dole Ki Zama Me Haƙuri Fiye Da Kowace Mace Amma Inba Haka ba Gidanki Zai zama Fagen Daga Sai kiga Kunfita Daban A Unguwa ƴaƴan Kuma Haka Zasu Taso.

Yadda ake zama da miji



Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYA


TAYAYA ZA A CANJA ƊABI'AR SAURIN FUSHI?

Aiki da ilimi da tarbiyyar muslunci sune kaɗai zasu saita mutum me yawan fushi, domin akan sami me tarin ilimi amma baya aiki da ilimin sai kaga da ransa yabaci ya tabka wani rashin ɗa'a.

Amma duk me aiki da ilimin sa da ranshi yabaci yayi fushi to zai nemi taimakon Allah sai kuga yaƙi yanke hukunci cikin fushi kamar yadda Manzon rahama s.a.w ya umarta.

Domin shi fushi Ɗabi'a ce ajikin rai baka da ikon hana kanka jinsa amma sai Annabin rahama yacema kazama me mallakar zuciyarka a yayin fushi.


Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA


YAKUMA HANAKA YANKE HUKUNCI A YAYIN FUSHI.

Dafatan mazaje masu saurin fushi da matansu zasu lura su rage su gane raunin dake tattare da su na hankali tunani hali da dakuma jiki.


Post a Comment

Previous Post Next Post