ABUBUWA 40 DAYA KAMATA KA KIYAYE YIN SU A RAYUWAR KA

 ABUBUWA 40 DAYA KAMATA KA KIYAYE YIN SU A RAYUWAR KA

Ba ko wani darasi ake koya da wahala ba a rayuwa, wannan yasa ake hana mutum aikata wasu Abubuwan.

Ana Hana ka aikata su ne dan kaima ka hankalta kar kayi kuskuren da wasu suka yi a baya.

Yana da Kyau ka Riƙe Waɗannan Abubuwan ka Sansu Yanxu.

1. KAR KAYI GULMAR WASU. Kayi Gulmar Kanka Maimakon Ƙarawa kanka zunubi.

2. KAR KAYI HASSADA. Kar ka yiwa kowa ƙyashi da Hassada. Idan Kana Hassada Rayuwar ka zata ƙare cikin Baƙin ciki, yayin da Zaka ga wanda kawa hassada yana Farin ciki, da Jindaɗi Sannan da Tarin Cigaba a rayuwa.

3. KARKA KAMANTA KANKA DA WAƊANDA SUKE FIKA. Kullum ka Rinƙa Kallon na ƙasan ka saboda anan ne zaka gane irin ɗaukakar da Allah Yayi Maka. Kayi Rayuwar ka kai kaɗai kawai kana duba inda kayi kuskure sai ka gyara.

4. KARKA TAKURA KANKA. Takurawa kai akan komai ba daidai bane. Kana aiki da Tinani.

5. KAR KAYI WA KOWA RASHIN KUNYA. Rashin Kunya Baya Taba Nuna Ƙarfin Mutum saidai Yasa ai maka kallon Shashasha. Ka Burge mutane da Ladabi shine zaisa a Girmama ka. 

6. KAR KA ZAMA MARAS TINANI. Duk lokacin da Kaji baka son abu kar ka faɗi mummunan magana akan shi. Ka bashi lokaci wataƙila kaso shi a gaba. Anan ne zaka gane kayi kuskure ko Bakayi ba.

7. KAR KAYI SHAKKAR KANKA DA YAWA. Idan Kasa Kanka zaka iya. Ka ɗauki kanka mai Ƙwaƙwalwar tinani daban data dabba. Duk abunda kaga wani yayi, kar kace bazaka iya ba, kawai bakasan yadda za kayi bane.

8. KAR KAJI TSORON AIKATA ABU MAI KYAU. Tsoro shine ke kashe zuciyar Ragwaye yake hanasu aikata abu mai kyau dan Goben su. Kafi Ƙarfin zuciyar ka kana aikata abu mai kyau.

9. KAR KANA BATA LOKACI MAI TSAWO AKAN KAFAFUN SADA ZUMUNTA (SOCIAL MEDIA). Tabbas Social Network suna daga cikin Manyan Wuraren Isar da Saƙonni, Labarai masu kyau, da ababen dariya. Amma karka bata lokaci mai yawa akan su.

10. KARKA RENA KAƊAN. Idan kana neman Wani abu mai yawa karka rena kaɗan ɗinshi ko taya yazo maka, domin idan ka tara kaɗan zai zama mai yawa.

11. KANA HAƊA IDANU DA MAI MAKA MAGANA. Ka gida Eye Contact da mutum yayin da yake maka magana hakan zai sa yaji kana sauraron shi kuma ka bada hankali akan maganar.

12. KARKA HANA KANKA BARCI. Kayi bacci aduk lokacin daka ji kanason yin baccin. Samun bacci Isheshshe kuma akan lokaci yana Taimakawa Ƙwaƙwalwa yin aiki yadda ya kamata..

13. KARKA YASAR DA ABUNDA KA TINA. Koda yaushe ka samu ɗan ƙaramin Papet da Abun Rubuta a tare dakai. Duk lokacin da wani abu mai amfani yazo tinanin ka ka rubuta shi kar ya wuce ka. Ba lallai ka iya tinashi daga baya ba zai bace maka.

14. KARKA ZAUNA DA ABOKAI MAGULMATA. Zama da abokai masu yawan surutu maras amfani baida amfani domin bazaka amfana da komai ba. Ka zauna da abokai wanda zasu taimaki Ilimin Ka Da Tarbiyarka.

15. KARKA KASHE LOKACI WURIN YIN ABUN MARAR AMFANI. Kasan Muhimmancin Lokaci a Rayuwar ka. Karka Zauna ba abunda kake. Kayi Karatu, Kayi Tinani, Kayi Aiki Sannan Kayi Ibada Kamar Kobe Zaka Mutu.

16. KANA YIN WASANNIN MOTSA JIKI AKAI AKAI. Yawan Motsa jiki yana yaye Damuwar Zafin Kai, Yana Daidai ta Lafiyar Jiki dana Ƙwaƙwalwar ɗan Adam. Sannan yana sanya Nitsuwa.

17. KARKA NA CHANJAWA ABU MEKYAU LOKACIN SHI. Musamman abu mai amfani to ka yishi lokacin da ka sanya. "The sooner you start moving toward your dreams the sooner you will enjoy the results of this journey."

18. KARKA DAINA KARATU. Ilimi Nada Muhimmanci. Idan Baka son a Barka a Baya, Kana Buƙatar Cigaba da karatu ba tsayawa domin Sanin Sabbin Fasaha.

19. KANA YAWAN MURMUSHI. Murmushi Sadaƙa ce. Murmushi na Firgita Maƙiya. Murmushi na Wanzar da Zaman Lafiya. Murmushi na Chanja Mutane.

20. KAR KACE KOMAI SAI KA IYA. Wani abun ka barwa Ikon Allah. Ka yarda akwai abunda bazaka iya ba. Wani Lokacin Saika Rasa Kake Samu.

21. KARKA RENA MUTANEN DAKE KUSA DAKAI. Duk wanda ke cikin Rayuwar Ka Yanada Muhimmanci, Duk abunda sukai maka ka Gode Musu.

22. KARKA BAR ƊAN KARAMIN DALILI DAN GUDUN DANASANI. Duk Ƙanƙantar Kuskure, Kaɗau Mataki saboda a gyra gudun faruwar haka nan gaba.

23. KA TAFI DA ZAMANI. Chanji Yana Ƙunshe da Sabbin Damanmaki, Riba da Kuma Cigaba. Ka Karbesu dan Kaima ka chanja naka rayuwar.

24. KARKA KARAYA WAJEN CIMMA BURI. Tinkarar Damuwa shine maganin Damuwa. Domin Cikar burin ka, ka tinkari Matsalar ka Da Burikan ka.

ABUBUWA 40 DAYA KAMATA KA KIYAYE YIN SU A RAYUWA


25. KARKA NUNA DAMUWA A IDON MAƘIYA. Kayi Ƙoƙari Ka Boye Damuwar ka dakuma Gajiyawar ka daga Idon Maƙiyan ka. Abunda suke so kenan. A Maimakon haka Kayi Murmushi.

26. KAR KAYI GULMAR KOWA KO KOMAI KODA KASAN KOMAI AKAN SHI. Yanxu mutum ake kiyo. Idan kana yawan Faɗe Faɗen Maganganu akan Wani to Mutuncin ka zai zube. 

27. KA KULA DA IYAYEN KA. Aikin kane kula da iyayen ka kamar yadda kake kula da kanka. Domin Iyaye Iyaye Ne Ba'a Chanja su.

28. KARKA BOYEWA IYAYEN KA DA ABOKAN KA KOMAI AKAN RAYUWAR KA. Waɗannan sune kaɗai zasu iya fiddaka daka Cikin Mummunan Yanayi ko ƙunci idan Ka Faɗa.

29. KARKA SHA ƘWAYA KO GIYA YAYIN DA KAKE CIKIN DAMUWA KO KULLEWAR KAI. Aikata hakan Bazai Taimaka maka ba, saima ya ƙara turaka cikin duhu.

30. KARKA ƘIRA TSOHUWAR BUDURWAR KA A WAYA MATUKAR TACE KARKA YI. Kar kayi abunda mutun cinka zai zube. Ka tina ta barka ne ko ka Barta ne saboda wani dalili. Karka manta.

31. KARKA BAIWA MUTANE SHAWARI HAKA KAWAI. Ba Kowa ke karbar shawari be nema ba. Karka baiwa kowa shawari sai wanda ya nema. Bazasu ɗauke shi da Muhimmanci ba, ka bayar lokacin da aka karba.

32. KARKA FAƊAWA KOWA SIRRRIN KA. KAWAI KA BOYE. 

33. KARKA FAƊAWA KOWA KALMAR" I LOVE YOU" INDAI BA DAGASKE KAKE BA. Wannan kalmomi guda uku Suna da Muhimmanci a wurin wasu. Ba'a wasa dasu if you don't meant it.

34. Karka Ɗora Personal Hotunan ka akan Social Media. Batagarin Mutane na jiran Ka.

35. KARKA YIWA MUTANE FASSARA DA KAYAN JIKIN SU, FATAR JIKI, KO KUƊIN SU. Wannan duniyar tana chanjawa a ko wani second. Nothing is Permanent.

36. KARKA KALLI GAZAWARKA. Kayi tinanin taya zaka zama Mai Ƙarko.

37. KARKA ROƘI KUƊI. Kana da Damar neman na kanka. Ka mutunta kanka ta hanyar hana kanka Roƙo, amma ka kula da naka.

38. KAR KAYI ƘOƘARIN JUYA WANDA BAYA SON KA JUYA SHI. Zai Iya Zubda Mutuncin ka a Idon duniya. Kayi iko da Wanda kake da Iko dashi.

39. KA ZAMO NA KOWA. Kar kayi Gaba Da Kowa. Kar kayi Fishi da Kowa Ka zama Mai Yawan Dariya.

40. KAR KAYI WASA DA ADDINI. Ibada Shine Dalilin Zuwanka Duniya. Kayi Ibadah Kamar Gobe Zaka Mutu.

Post a Comment

Previous Post Next Post