HANYOYIN DA ZAKA BI KA SACE SOYAYYAR MACE
Babu shakka kowane namiji yana burin jin ana sonsa, musamman ta wurin abokin zamansa (Masoyiya). Soyayyar mace na bawa saurayi Ƙarfin gwiwa, domin cigaba da rayuwa mai tsafta.
Samun zuciyar mace yana buƙatar aiki mai yawa, Amma hakan zai yiyu ne idan har kabi wasu hanyoyi masu sauƙi. Sanin bambanci tsakanin mace da namiji a soyayya yana sa wannan lamari ya yiwu kuma canza wasu kalmomi na iya sanya mace ta so ka da gaske. A cikin wannan Rubutu, zan tattauna hanyoyi guda uku, idan ka bisu to kamar soyayyar ka ta karbu.
They include the following.
Compliment her (Yawan Yabon Ta)
Shin ko kunsan cewa yin yabo yana É—aya daga cikin mafi kyawun hanyoyin da za'a bi wajen samun zuciyar mace? Yawancin mata suna son jin kalmomi irin su Kina da kyau, kayanki masu kyau ne, ke mace ce mai hankali, da sauran kalmomin da ke nuna bayyanar Yabo na Soyayya, da halayenta. Yana kara mata kwarin gwiwa kuma yana faranta mata rai, kuma wannan farin cikin tabbas yana bayyana a fuakarta, har ma da zuciyarta.
Respect her feelings and don't underestimate them
(Ma'ana: Ka girmama yadda take ji (Shauƙi) kuma kar ka raina Abunda Take so.)
Saboda yanayin tausasawa na mata da yawa waÉ—anda suke Su Shgwababbu ne a mafi yawan lokuta, yana iya kaiwa ga yin kuka, domin akwai mata masu saurin kuka kana yi musu abu kaÉ—an.. Duk da haka, yawancin maza sun kasance suna raina wannan al'amari wanda kuma ba haka suke so ba. Koda yake wannan rauni ne na duk mace kuma sirrin karfinta yana cikin rauninta.
Dan haka duk mace mai irin wannan, tana buƙartar kome tayi kace yayi kuma ka yabi haka.
Spend some time with her (Ka Bata Lokacin Ka)
Idan Namiji da Mace suka jima suna hira tare, to hakan zai ƙarfafa Soyayyar su, domin yana tasiri sosai.
Kuma yana saka mace ta fahimci irin farin cikin da take shiga idan tana tare dakai. Kuma hakan nasa mace faÉ—awa Soyayya da Namiji cikin sauri.