YADDA AKE RARRASHIN BUDURWA

 HANYOYIN DA ZAKA BI KA RARRASHI BUDURWA.

A kowace mu'amala ta dangantaka ko soyayya, samun matsala ko yin faɗa tsakanin saurayi da budurwa, ko miji da mata ba baƙon abu bane. Idan kana fama da irin wannan matsalar da budurwar ka, to ga hanyoyi guda 5 da zaka bi wajen Ganin kun Shirya cikin sauƙi.

Afuwa: Idan ka yi wa budurwarka laifi ko ka 6ata mata rai, kuma kana son ta hakura, to ka yi hakuri ta hanya mai kyau da natsuwa ka fada mata dalilin da ya sa wannan laifin ya faru, kuma ka yarda ka aikata. laifin.

Karanta: ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA

 Lallai akwai wani abu da zaka yiwa mace domin mata basa fishi da namiji sai dai idan akwai ƙwaƙƙwaran dalili, kana iya ƙoƙarinka wajen ganin ta yafe maka ta manta abinda kayi mata domin kana sonta.


Na biyu 

: Ka saya mata kyauta: Wannan babbar hanya ce ta kawar da laifinka. Yawancin mata suna son kyauta, musamman daga mazan da suke so. Idan kun ɗan yi fada to ka saya mata kyauta kaje mata dashi. Zai sa ta manta cewa ba ka cutar da ita ba. 

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

Aika mata da Kalaman Soyayya masu Daɗi: Idan kayi Fada Da Budewar Ka Kuma Kana So Ku Shirya, To ka Rikita wayarya da Sakonnin soyayya, shima hanya ce mai kyau kuma tana kara danƙon soyayya, kuma kalaman soyayya suna sanya mata farin ciki sosai.  A cikin rubutun naka kayi ƙoƙarin bata hakuri. 

Ka dauki laifin, ko da ba laifinka ba ne: wannan wata hanya ce ta mu'amala da masoyiyarka, domin idan ka zargi kanka, ba ta da wani zabi illa ta yafe maka. 

Karanta: YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA

Wani lokaci mata da miji su kan shiga cikin matsala domin babu wanda ya yarda ya dauki laifin abin da ya faru a tsakaninsu, sai su zargi junansu.  Don haka idan kana da laifi ka daure ka karbi laifin, ka ba ta hakuri, ba Gajiyawa  ba ne a soyayya. 




Karanta: ABUBUWAN-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA


Ka Kasance Mai Gaskiya: Kayi ƙoƙari wajen faɗa mata gaskiya a duk abinda zakace mata, kuma kayi haƙuri da abinda take aikatawa. 

Gaskiya abu ne mai kyau a cikin soyayya, kuma idan kuna faɗin gaskiya ba za ku sami matsala sosai ba. 

Muna godiya da gudunmawar ku masoya.  Kar ku manta kuyi sharing tare da Like domin wasu irinku su amfana da nasihar mu akan soyayya.


Post a Comment

Previous Post Next Post