YADDA ZAKA NUNAWA MACE SOYAYYA
Idan ka samu mace da kake so kuma take son ka. Abu yayi kyau. Indai kana Son Soyayyar ku ta kasance Mai tsawo kuma har kuci ribar ta, to akwai wasu hanyoyi da ake bi. Idan har ka iya bin waɗannan shawarin to kai da Budurwar ka zaku yi Soyayya mai Daɗi kuma cikin Annashuwa da farin ciki.
Waɗannan Abubuwan suna da kyau a zamantakewa ta Soyayya, suna ƙara ƙarfin Soyayya fiye da tsammanin mu idan har muka bisu.
1. Be kind (Ka Zama Mai Tausayi?
Tausayi Kaɗan na tafiyar dogon zango. Idan ka nuna tausayin ka ga masoyiyar ka zata ji daɗi, misali idan kayi mata wani kuskure kaɗan to kace mata Kiyi Hakuri, Idan tayi maka abu kaji daɗi kace mata NAGODE, you're Welcome, da dai sauran su. Sannan Ka yawanta yabon ta Hakan yana da tasiri sosai.
2. Connect daily (Kana Yawan Connecting da Ita a Rana)
Meme dame ya faru yau HubbyNa. Ba kunya acikin tambayar ta game da wunin ta, ka kasance koda yaushe kana jin me yake faruwa da ita da ƴan uwanta, hakan na ƙara danƙon Soyayya mai ƙarfi. Yawan ta yi mata text kana tambayarta kina lafiya, ba wata matsala? Zai sata jin cewa ka damu da ita.
Duk lokacin da kuke tare, lokaci ne kuka samu domin bayyana abunda kuke dashi a xuciya, ka riƙe Hannun ta ka kalli cikin idanuwan ta domin tabbatar da ƙaunar ka gareta.
Farin cikin da Soyayya ke bayarwa tana ƙara lafiyar jiki sosai. Sannan yana ɗebe damuwa da baƙin ciki daga zuciya.
Karanta: YADDA-AKE-HIRAR-SOYAYYA-FARKON-HADUWA
3. Express gratitude (Kar Kaji Kunyar Faɗa Mata Me Kake So)
Ka Saba Yabon ta, duk abunda yake burge ka a jikin ta, ka yabeshi yayin da kake kallon idanuwan ta, Kayi godiya abisa Soyayyar data baka, Ka sake godiya abisa Fahimtar data yi maka.
Ka ƙirƙiro wasu hanyoyi na daban wanda take so kana yi mata su kullum, kamar saka ta dariya, Tsokana da sauran irin su.
4. Plan a surprise (Kana Mata Bazata)
Kana Yi mata kyautar bazata, bawai flowera ne kawai mata keso ba. Akwai wasu Nau'in abubuwa da mata keso, irin su kayan zaƙi, kayan kwaɗayi. Kada ka kai mata shi haka, ka sanya shi cikin Wrapper. Mata suna son irin wannan.
5. Support their dreams (Kana Nuna Mata Kana Son Abunda Take So)
Idan Kana Son mace, to zaka kula da abunda take so. Ka zamo kaina na farko wajen Goyon bayanta akan abunda take so. Ka kasance mai bata shawari wajen gudanar da abunda take so. Kada ka nuna bakason abunda take so, Soyayyar ka zata shiga matsala. Inda Hali Nuna mata Hanyar da zata cimma wannan Mafarkin Nata wato Burinta kenan.
Duk abunda zaka yiwa mace idan ka kasance da ita a jam'iya ɗaya to wannan abunda yafi mata komai. Zata baka Soyayya, ta baka kulawa, ta baka lokacinta. Kuna zata Girmama ƙudurin ka cikin hanzari.
Girmamawa Yana daga cikin abunda maza ke so amatsayin Soyayya.
6. Jealousy (Kana Nuna Kishi akan Ta)
Duk abunda zatayi ya ɗau hankalin wani bakai ba, to kayi ƙoƙari wajen nuna mata kishin ka, ka nuna mata baka son wannan abunda Amma cikin hikima. Mata basu cika damuwa da irin haka ba, dan basa iya ganewa cewa Abunda suke zai iya batawa Saurayin ta rai Saboda Kishi.
It is a sign of them being invested in you; so when you show jealousy in a positive way it demonstrates to the other person that you care most.
Kai Kuma ka nuna kishin ka ta hanyar data dace, kada kace zaka nuna Izza Da Fin ƙarfi. Ka nuna mata kishin ka cikin Soyayya, ta yadda bazata gane kana mata umarni ba.
Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA ME KWAƊAYI
7. Seek advice (Kuna Shawari)
Amatsayin ka na saurayi ka kasance mai yawan yayewa mace damuwarya. Kasan Yadda zaka bata shawari mai kyau. Ka zamo Bolar damuwar ta, duk wata matsala idan tazo maka dashi ka Magance mata shi.
Hakan zai saka ka zamo Na farkon nema da zarar damuwa ta same ta. Sannan kana neman shawari a wurin ta kaina, hakan zai saka ta jin itama tanada wani rawa da take takawa acikin rayuwarka.
8. Give your undivided attention (Ka Bata Lokaci)
Mallakawa mace lokaci Shine sirrin duk wani aminci da zaka samu daga wajen mace.
Mace tana bukatar lokacin ka sosai idan kana son ta fahimceka, da wannan lokacin ne zatayi amfani dashi wajen gane Soyayyar ka gareta.
Karanta: AMFANIN AUREN MACE DOGUWA
9. Dress to stir desire (Shiga Mai Kyau)
Kuna yin shiga mai kyau idan zaku haɗu, ko wannen ku ya ƙure adakar shi wajen burge ɗan uwanshi. Kuyi ado da kwalliya mai kyau na gani na faɗa.
Kiyi kwalliya musamman saboda shi, kayi kwalliya musamman saboda ita hakan zaisa yaji shima yana da gata a wurin ki. Idan namiji ya ganki a yanayin da yake yana ganin ki, musamman idan kun jina kuna tare to akwai wani saƙo da hakan ke bayarwa na musamman wa Soyayyar ku.
10. Love without conditions (Kayi Soyayya Bada Dalili Ba)
Idan Kana son mutun Kaso Shi bada wani dalili ba shine Soyayya. Duk dalilin da zaka bayar dan ka nuna kana son mace wataran wannan dalilin zai iya gushewa ka nemeshi ka rasa. Daga nan Soyayyar ka ta shiga garari.
Fatan Nasara a Soyayya 🙏🏻