YADDA ZAKA GANE SOYAYYAR GASKIYA DANA KARYA.

MANYAN ALAMOMIN SOYAYYA TA GASKIYA


Tun kafun a haifeka ake Mafarkin neman Soyayyar gaskiya. Hatta mutanen da basu yarda da Soyayya ba suna son Soyayyar gaskiya. Amma Saboda Ɗaya daga cikin Burin Ɗan Adam shine Samun Soyayya ba shine yake nuna Ansan menene Soyayyar gaskiya ba. Akwai Soyayya kala kala akwai na Kirki Akwai na Banza. Saboda rashin tabbas ɗin samun Soyayyar gaskiya yasa wasu basa son ma su kusance ta.

Amma Idan har ka Samu wani wanda yake sonka da gaske, to karka bar Soyayyar Shi ta tafi a banza. Saboda haka, Kana Buƙatar koyon yadda zaka gane Soyayyar gaskiya. Idan kana daga cikin Mutanen dake tsoron Soyayya, to Zaka Samu Ƙarin Ilimi anan Wanda zai Chanja maka Rayuwa. Yana daga cikin Yin Rayuwa mai Ma'ana dakuma daɗi Shine ka samu Soyayya ta gaskiya mai Daɗi.

Zaka Iya Soyayya da mata da yawa a rayuwar ka, amma taya zaka gane wacce ke sonka da gaskiya? Ga wasu kaɗan daga alamomin da zakaa gane mai sonka da gaskiya.:

Alamomin Soyayyar Gaskiya:

1. Rashin Fargaba da Tsoro.

Daga cikin alamomin Soyayyar gaskiya akwai Rashin Tsoro ko Fargaban kada wani yayi maka shigan Burtu, ko tsoron Kada Wacce kake so ta yaudare. Idan Har Ka samu kanka a yanayin Da Komai ka Yarda da masoyinka Baka Tsoron zai Gujeka Ko Zai Maka wani abunda zaisa ka barshi, to wannan Na daga Cikin Alamun Soyayya ta gaskiya.

Duk Jinawar Da za kuyi da mace indai baka jin ta isheka, ko baka jin Soyayyar ta na raguwa daga zuciyar, Kullum saidai kaji Ƙaunar ta na Ƙaruwa Shauƙi Kullum na daɗuwa to wannan Shine ake buƙata. A Soyayya koda bakwa wasanni ko tsokana wa junan ku amma kuma kuna son juna kuna martaba juna kuna kiyaye haƙƙin Soyayya to Kuna cikin Soyayya ta gaskiya.

2. Koda Yaushe Kuji Kuna son Zama Kusa da Juna.

Idan Har Soyayya Tayi Ƙarfi kuma tayi daɗi, masoya suna mararin juna ta hanyar son Zama inda masoyi yake kuma suɗau Tsawon lokaci tare ba tare da Sun Gundiri juna ba, batare da Ɗaya najin Haushin Ɗaya ba, Sannan Duk jimawar da za suyi Zaka gansu cikin Murmushi da dariya, kuma Ba'a son Rabuwa, to wannan alama ce ta Soyayyar gaskiya. 

Duk Soyayyar da Kullum zaka ga Farin ciki na ƙaruwa ba tare da ya dishe ba, ko kaga duk irin Shaƙuwar da kukai Bakwa yin wani abu da zai bata Soyayyar ku to alama ce ta Soyayyar gaskiya.

Yana Da kyau kasancewa kusa da masoyin ka koda cikin taron Jama'a ne. Kawai kaji kai koda yaushe kafison zama kusa da budurwar ka, idan kun haɗu bakwa son rabuwa koda kuwa Kullum ne. Koda Zaka tafi wuri mai nisa duk Muhimmancin shi amma kaji kaifa zama kusa da ita yafi maka farin ciki da Shauƙi.

True love


Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYAR GASKIYA

3. Kuji Kuna Son Juna Koda Halinku Ya Banbanta.

Ko wani mutum yana da wani halayya wani ya maida shi na daban acikin mutane. Sannan wannan halin kuma shine zaisa ba kowa ne yakeson zama kusa dasu ba. Misali, Kai mutum ne mai yawan Ɗaga Muryar idan Kana Magana, wannan wasu basa son haka, Abokan ka da ƴan uwanka ne kawai zasj iya zama dakai a haka. Amma zasu faɗa maka ka rufe bakin ka wato kana magana ƙasa ƙasa.

Amma idan ana Magana akan Soyayya ne, wasu masoyan rabuwa suke idan rashin jituwa ya shigo. Idan Har ka samu masoyin gaskiya to duk yadda kake zaiji kawai ka masa a haka. Harma zaka ga masoyin naka shi zai taya ka ku gyara abunda kake batawa. Wannan Shine Soyayya ta gaskiya.

4. Kuji Kuna son Ɗayan Ku Yayi Nasara.

Kaji kana son Masoyin ka Yayi nasara a komai da yasa a gaba don cimmawa. Kaji ka ƙagu kana so, Zaka iya jin zafi idan baiyi nasara ba to wannan Alama Ce ta Soyayyar gaskiya. 

Idan har ka kasance Wanda yake son cigaban masoyin shi amma baka Taimaka mishi ta hanyoyin da suka dace to wannan ba Soyayya bace. Soyayyar gaskiya shine ka tallafawa masoyin ka wajen Cimma burin shi na rayuwa.

Karanta: HANYOYIN-MALLAKE-USTAZAI-MAZA-DA-MATA

Idan Har Kana Soyayyar gaskiya zaka iya yin duk abunda ya kama kayi wajen nemowa masoyin ka abunda ranshi keso batare da ka gajiya ba. Zaka iya sadaukar da naka farin cikin domin nashi.

Soyayyar ku zata Kasance Akwai Fahimtar juna, Akwai Goyon Baya, Sannan Akwai Soyayya daga Duka Ku Biyun. Zaku Girma tare Soyayyar ku Tayi Ƙarfin da Zaku kai ga Aure.

5. Jurewa Zafi, Damuwa, Ƙunci da Sauransu.

Mutane da Dama Yana wahala Su iya Fuskantar Damuwar su. Koda Suna Cikin Dangi Da Abokai. A Soyayya Ana Son ka zamo mai jurewa duk wata rayuwa ta wahala ko Ƙunci da damuwa.

Idan Har ka samu wacce kake so da gaskiga, za kana buɗe mata zuciyar ka, bazaka boye mata komai ba. 

Ba komai ake Boyewa a Soyayya ba sannan ka zamo mai Hakuri yana bawa Soyayya tasiri mutunci da Shauƙi.

Sannan bazaka na jin kunya ko Tsoron Faɗawa Masoyiyar ka damuwar ka ba, haka Itama bazata boye maka komai ba.

6. Za Kana Mafarkin Rayuwa Mai Zuwa.

Idan Kana Yin Soyayyar gaskiya zakana Tsammani ko Rayawa a ranka cewa nan Gana Ga yadda zaka kasance da Ita, Sannan Zaka kana rayawa ga yadda rayuwar auren ku zai kasance. Sannan Duk wani Plan na Rayuwar ka zakana sakata a ciki. 

Idan Mutum biyu na Soyayya ta gaskiya, Baza suji kunyar yin Irin Waɗannan Tinanin ba. Da kanku zakuna gina irin rayuwar da za kuyi nan gaba ko nan da wasu shekaru.

Karanta: HANYOYIN DA AKE BI A DAINA ISTIMNA'I (Masturbation)

Rufewa

Soyayyar gaskiga wani abu ne da kowa ya samu yayi dace. Ba kowa ke samun damar kasancewa da Soyayyar ba. Sannan ba kowa ke son Faɗawa wani sirrin shi ba. Sannan akan iya rasa Soyayya gaba ɗaya idan har bata gaskiya bace. Idan Har kana kokwanto akan Soyayyar ka karka bari shakka ya bata maka ita.

Yin Soyayyar gaskiya na Nufin son zama kusa da juna, son sanin komai akan wanda kake so, Son Cimma buri ko Son Masoyin ka ya samu abunda yake so, kayi sadaukarwa domin farin ciki. 

Kaso Wani abunda take so, Ka kauda kai akan halaye maras kyau. Kaso ku kasance tare A Lokuta masu zuwa. Kuyi aiki tuƙuru wajen cimma burin ku Tare.


YADDA ZAKA GANE SOYAYYAR GASKIYA DANA ƘARYA.


Mutane da dama suna faɗawa tarkon Soyayya, kafun su farga an yaudare su, kafun haka ta faru yakamata ka natsu ka karanta waɗannan alamomin domin tantance Soyayyar gaskiya daga Soyayyar ƙarya.

1. Duk Macen da bata Iya Kallon idanun ka, ko namijin da baya iya kallon cikin idanun ki. Wannan babbar alama ce ta Soyayyar gaskiya. Akwai kunya a Soyayya.

2. Duk Soyayyar social media irin wacce bata yadda kuyi Video Calls ko Ta turo maka hotunan ta, kawai ka daina kusantar irin waɗannan domin akwai yaudara aciki. Za suyi amfani dakai ne kawai yayin da suke buƙata, suna kammalawa kuwa shikenan.

3. Idan kuka fahimci Mace tason yawan taba jikin ɗa namiji, ko namiji yana yawan taba jikin ƴa mace, ko son Su kwanta tare da sunan Soyayya, ko Irin Soyayyar #besty, to dama hausawa sunce "Ruwan Kashe Gobara Ba sai me Kyau Ba" Idan kanason kayi rayuwa mai tsafta kuma mai daɗi to ka guji iri. Waɗannan, ko ki guji irin waɗannan samarin.

4. Duk wanda zai iya sadaukar da wani abu nashi wanda yake so saboda ke ko kai, to Wannan mutumin ba abun yasarwa bane. Ko ya aikata wani abu mai girma don kawai yasa ki farin ciki. 

5. Idan Har Baya iya Shiru Akan Kuskuren ki, ko ta zama bata iya jure kuskuren ka, ko yawan tinawa da wani Kuskure na baya, abokina ka fece kawai. Bayan kun rabu sukan iya amfani da Wannan kuskuren wajen BlackMailing naka.

6. Idan Kaga mace bata damu data rasaka ba, ko kika ga namini bai damu ba dan ya rasaki, Wannan Soyayyar ƙarya ce. Ko Taɗau dogon lokaci batare da taji ɗuriyarka ba, kuma bata damu ba, ka manta da kashin Wannar Soyayyar.

7. Idan yakasance komai saidai kai mata, ita bazatai maka ba, to Soyayyar ƙarya take maka. Duk wanda yake sonka da gaske zai iya yin komai don farin cikin ka. Mace ko Namiji.

8. Duk Namijin dake yawan maganganun Batsa, ko mace, to ba abokin zama bane na gari. Wasu matan sukan yi haka idan har suna son wani abu a wurin Namiji musamman kuɗi. Kawai za suyi amfani dakai ne na ɗan wani time, yayin da kaikuma zakai tinanin sonka ake.

9. Idan Ta fara kamantaka da wani saurayi daban..... Duk wanda zai soka to kaine mafi Soyuwa agareshi. Ba wani can gefe ba.

10. Zaka ga suna riƙe Soyayyar ka da gaske, ko wani sirri naka kuma basa so wani ya sani koda Family ne, to wannanr Soyayyar gaskiya ce.

11. Idan kaga mace bata son jimawa dakai ana hira. Sorry My Friend. 

Post a Comment

Previous Post Next Post