YADDA ZAKA KAUCEWA YIN FAƊA A SOYAYYA

 YADDA ZAKA KAUCEWA YIN FAƊA A SOYAYYA

Duk wani Soyayya komai daɗin shi ko ingancin shi, watarana zai iya fuskantar rashin fahimta ko samun sabani. Wannan yana faruwa ne saboda mu mutane haka Allah yahalicce mu Ra'ayin mu daban. Hakan yana faruwa ne idan wasu abubuwa suka faru cikin zamantakewa ta rayuwa.

Idan ka tsinci kanka acikin Soyayya da wacce kullum take fifita buƙatun ta akan naka, to kana buƙatar neman wasu hanyoyi domin ku zauna lafiya da halinta.

Acikin wannan rubutu zanyi magana akan wasu abubuwa biyar amma ataƙaice ta yadda zaka kaucewa faɗa acikin Soyayya ko Aure.

1. Duk yadda kuke Soyayya da kulawa da juna, akwai wani lokaci da Ra'ayin ku zai iya banbanta, whether consciously or unconsciously. Sannan ranka zai iya baci saboda wani abu da tai maka ko ta faɗa maka. Idan irin haka ya faru yana da wuya mutum gane yadda zai shawo kan lamarin. Maganin hakan kawai shine hakuri tare da kai zuciya nesa. 

Koda wasa kada kuyi kuskuren faɗawa wani tsakanin ku komin shaƙuwar ku da mutum. Sirrin ku naku ne.

Karanta: YADDA-AKE-HIRAR-SOYAYYA-FARKON-HADUWA

3. Idan ya zaman cewa masoya biyu basa iya ɗaukar darasi daga wani abu daya faru ga na kusa dasu, to sukan iya faɗawa irin wannan matsalar. Yana da kyau idan kaga abu ya faru da wani naka to kaima sai ka ƙirƙiro wata hanya da zata taimaka maka wajen kaucewa faɗawa irin wannan matsalar.

Yana da kyau ka san yadda masoyiyar ka take kallon rayuwa, me ta yarda dashi, me take so, me bata so, hakan zai taimaka sosai wajen yaɗuwar farin ciki.

Karanta: ILLOLIN-AUREN-MACEN-DA-BATA-SONKA

3. Ku kasance da natsuwa yayin da kuke mu'amala da Masoyan ku Miji ko Mata, musamman idan suna cikin damuwa ko tsoro. A wannan ana buƙatar natsuwa sosai tare da sassanyar murya da kalamai masu daɗi na kwantar da zuciya. 

Ku tuna cewa mafi kyawun mayar da martani ga tashin hankali shine zaman lafiya; a sakamakon haka, ya kamata ku yi ƙoƙari don samar da zaman lafiya maimakon maiyar da martani ga junan ku.





Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DA MAZA KE SO A JIKIN MATA


4. Yana da kyau bayyana Abubuwan da ba daidai suke tafiya ba domin a dai-dai tasu. Yana da kyau koda yaushe kuna tambayar juna saboda ɗan adam yana canjawa. Me kikeso me nake yi miki wanda bakya so domin na gyara. Haka itama matar. Amfanin yin haka shine gudun danne haƙƙin ɗaya daga cikin ku, don ku nusar da farin ciki tsakanin ku.

Karanta: YADDA ZAKAYI MACE TA YADDA DAKAI 100%

5. Kada Kana Yiwa matar ka ZATO akan abunda baka so Kuma tana yi, domin shi zato yana wargaza gaskiyar lamari komin ktauwun shi. Domin gujewa tashin hankali ko 6acin rai, ka fito fili ka faɗa mata kaifa abu kaza mai maka ba a gyara. 


DuniyarLove❤

Post a Comment

Previous Post Next Post