HANYOYIN MALLAKE USTAZAI MAZA DA MATA

HANYOYI GOMA NA MALLAKE USTAZU KO USTAZIYA 

Da Farko Wanene Uztazu??

Ustazu ko Uztas Yana nufin wani mutum ne wanda ya kame kanshi da niyar aikin neman ilimi ko karantarwa, shi ba irin normal mutum bane, duk wani abunda bana addini ba baya cikin shi, komai idan zeyi to saiya jawo Ayar Qur'ani ko Hadisin Annabi (S A W). Bai cika yadda yana yawan mu'amala da Mata ba sai dai idan sunzo neman ilimi. 

Haka Yake a Bangaren Matan Ma, Saidai Su Sukan Killace kansu ne acikin gida, ko ƙawaye basa tarawa, basa yawan fita koda kuwa zuwa aika ne balle ma su saba da mutane.

YAYA ZAKIYI IDAN KIKA SAMU USTAZU KINA SO?

YAYA ZA KAYI IDAN KA SAMU USTAZIYA KAN SO?

Ku karanta A Natse Tare da Fahimtar ko wani wasali domin Morewa Soyayyar Ustazai:

1. Kuyi addu'a sosai kuma kinace da Addu'a

Ita Addu'a Dama makami ce ta duk wani mumini wajen neman abunda baya dashi ko ya rasa. Kuma ita Addu'a sai anyi naci sannan a tabbatar an iya addu'ar domin itama sai mutun ya ƙware.


Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

2. Ki zama ustaziya acikin mu'amala mai kyau da Shiga me kyau.

Mafi yawancin matan mu na yanxu sun biyewa zamani basa duba makomarsu ya zata kasance, shiyasa suke abubuwan da ustazan basa ma Sha'awar su balle suce suna so. Amma indai kina son ustazu kema sai kin zama ustaziya koda dan Soyayyar da kike mishi ne.

3. Ki zama mai kyawawan É—abi'u  da tarbiya ta musulinci.

Matuƙar kina son ustazu to yana da kyau kiyi Mu'amala dashi irin wacce zata ja hankalin shi gareki, sannan ki zama ta kirki, ki iya Karatun Qur'ani Da Hadisi koda Ba Yawa Kinci Gari.

4. Ki zama mai aiki da Abunda kika koya.

Kada kina koyon Karatu kuma bakya aiki dashi, ko a wurinshi kike koya to yaga cewa lallai kina aiki da Abunda ake koya miki.

Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA

5. ki zama mai kunya, tsafta, nutsuwa, iya magana.

Idan har kika iya Sarrafa Kunyar ki to zaki fece da zuciyar ustaz, Nitsuwa zata taimaka miki kwarrai, Ki haÉ—a da Iya Zance musamman iya hira da Surutu amma mai Kan Gado ba na shirme ba.

6. Ki zama kin shagala da Neman ilimi addini da na boko

Koda Kin shagala to kada Ki Manta Da cewa ke ustaziya ce yanxu ustazu kike nema dan haka Bokon ki kada ta saki girman kai, ustazu baya son girman kai.

7. Ki zama mai taimakawa ummah wajen wanke-wanke da girke-girke.

Duk lokacin da Ustazu ya fahimci kina yawan Taimakawa mom wajen aikin gida zai gane cewa lallai kina taimakon iyaye dan haka zaki iya kula da Miji. 

8. Ki zama mai Neman addu'ah wajen iyaye da mutanen Kirki.

ZUCIYAR ustazu fa bata samuwa ta daÉ—i sai an zage damtse an kwana akan buzu sannan an tambatar ana aiki da Jiki.

Karanta: DABARU 15 DA MAZA KE AMFANI DASU

9. Ki zama mai kamun kai acikin 'yan uwanki mata.

Ko Me zai kasance tsakanin ku da Ƙawayen ki to kada ki saki jiki wajen rashin kamun kai, ko ina Kike ki nuna kefa kina da mutuncin ki, da kamun kanki.

10. kizama mai sutura ta addini 

Munyi Magana Akan shiga Me kyau a Baya, sai a Kula

Insha Allahu idan kika kasance mai wannan halaye shi da kansa ustazun zai ta Addu'a don Allah yabashi ke.

Post a Comment

Previous Post Next Post