YADDA AKE HANA MATA YAUDARA A SOYAYYA

 HANYOYIN DA KAUCEWA YAUDARA CIKIN SAUƘI


Kuna mamakin yadda zaku bayyana soyayyarku ga masoyan ku? Lokacin da kuke bayyana ƙaunarku ga waƴanda suka cancanta, yana sa ku biyu kuyi farin ciki. Hakanan zai zaburar da wanda kuke faɗawa, suma suji suna ƙaunar ku. Ba wani abun boyewa bane dan kana son mace kuma ka boye, haka suma matan. Idan kana son ta, ko kina son shi. Ku bayyana.

Ga Hanyoyin da zaku bi don bayyana yadda kuke ji akan masoyan ku.

1. Ka dinga Yawan haɗa idanu da ita. Idan kana haɗa idanu da mace yana sa mata zargi, amma idan haɗa idon yayi yawa to zata fara tinanin akwai wani abu a ƙasa. Lokacin da zata faɗi haka kuma to ka riga da ka gama mamaye mata zuciya. Domin tinanin ka zai auri ZUCIYAR ta daga nan ka samu shiga.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

2. Zaka iya rubuta mata Wasiƙar Soyayya mai tsawo. Rubun Hannu a paper yana da amfani sosai. Amma idan baka son Mata rubutun hannu, zaka iya tura mata saƙo ta Waya wato Text, ko ta Email. 

Rubuta wasiƙa mai tsawo zai baka damar bayyana duk abunda yake ZUCIYAR ka, da duk wani feelings naka. Kuma ga karanta Wasiƙar, zasu fahimce ka cikin sauƙi.

3. Fahimtar Masoyi ko Sauraran Maganar masoyi. Idan kuna bata tsawon lokaci tare, to zaku fahimci juna sosai kuma ta hanyar data kamata. Idan kuka fahimci juna, to kun ɗauƙo hanyar gamsar da junan ku da Soyayya.

Masoyiyar ka ko Masoyin ki. Suna da abun faɗa da dama zuwa ga masoyan su. To Ba'a son boye zance.

4. Ka zauna da masoyin ka acikin daɗi ko rashin sa. Ka tabbatar wa masoyin ka cewa zaka tsaya mashi acikin duk wani yanayin daya samu kanshi. Shima hanya ce ta nuna Soyayya.


Yadda ake hana mata yaudara


5. Kana yawan bata kyauta mai Ma'ana Duk bayan wasu lokuta. Yakamata kana bada tazara wajen bata kyauta. Kada ka rakura kanka wajen kashe kuɗaɗe akan ta. Abunda kawai za kayi shine ka samu abunda take so komin tsadar shi ka saya mata sau ɗaya a cikin wata ɗaya ko wata biyu.

6. Kayi matuƙar nuna kulawar ka garesu lokacin da basu da lafiya. Idan Budurwar ka bata da lafiya, kana buƙatar nuna jajircewa sosai wajen nuna ka damu da damuwar su. Sannan ka nuna Soyayyar ka garesu a wannan lokacin. Mata na son irin haka.

Post a Comment

Previous Post Next Post