ZABABBUN KALAMAN LOVE

 ZABABBUN KALAMAN SOYAYYA

Zafafan kalaman Soyayya tare da kalaman love, wato Soyayya text Message, sune muka haɗo tare da Kalaman Soyayya zafafa kuma na musamman domin ku masoya.


 1. 1. Asalin Abinda Nakeson Rubutawa Yana Zuwane Cikin Yanayin Kallon Abinda Idona Ya Kallato Daga Kyakkyawar Fuskarki. Nasabar Asali Gamida Tsaftatacciyar Halitta Wadda Take ɗauke Da Dukkan Wani Kwarjini Mai Busowa Cikin Shauƙin Annashuwar Fuskarki Adaidai Lokacinda Kike Gabatar Da Murmushi Agareni
 2. 2. Inason In Baki Labarin Cikin Zuciyata Saidai Har Yanzu Nakasa Samun Nutsuwar Gabatar Da Hakan Sakamakon Yanda Sonki Da Tunaninki Ya Mamaye Dukkan Zuciyata. Soyayyarki Ce Aikin Cikin Ruhina Yaya Zanyi Ne Idan Na Wayi Gari Banji Motsi Kokuma Sauraron Muryar Data Fito Daga Gareki Ba
 3. 3. Kyakkyawan Kusancine Tsakanin Zuciyata Da Taki Shiyasa Bana Fahimtar Dukkan Wani Zance Wanda Bai Samo Asali Daga Zuciyarki Ba. Aminci Agareki Ya Abun So Da Sadaukarwar Ruhin Jikina Kece Madakatar Dukkan Wasu Zantukan Cikin Zuciyata Inasonki
 4. 4. Bayan Kammaluwar Sallama Daga Masoyi Zuwa Gurin Abun Sonsa Sai In Gyara Zama Domin Samarwa Kalamaina Masauki Acikin Fadarki
 5. Idan Nayi Dace Sarauniya Ta Dubi Zantukan Zuciyata Lallai Sai Inyi Tsalle Da Murna Ganin Yanda Nasamu Nasarar Samun Abinda Na Dade Inaso
 6. Kyawun Zubin Sura Gamida Tsaftataccen Halin Mutanen Kirki Kin Samo Asalinsu Ne Tun Daga Iyaye Shiyasa Komai Naki Yake ƙara Bayyana Da Cikar Asalin Girman Dakika Samu Daga Gidanku
 7. Ban Fara Sonki Da Wasa Ba Dan Haka Bazan Daina Shi Koda Wasa Ba Ni Sonki Nake Da Dukkan Zuciyata
 8. Amincin Allah ya tabbata agareki dafatan kina lafiya haƙiƙanin gaskiya kinada kyau kuma hasken idanuwan ki sukan ɗauke hankali kaman yadda daɗin muryarki yakan kwatar da zuciyar mai sauraro nagodewa Allah daya bani ke.
 9. Tabbas so halittace Burin zuciya na bai wuce namallakeki ba, Burin ƙafafuna su zo gareki Burin Idanuwa na shine su kalli kyakkyawar fiskarki.
 10. Haƙiƙa nayi dace dasamunki arayuwa kin zama farin cikina da sonki nake kwana kuma ki sani dashi nake tashi karki manta ni mai ƙaunarki ne idan na rasaki rayuwa bazatamin daɗi.
 11. Zafafan kalaman soyayya
 12. Samunki arayuwata ya samar da wani gagarumar chanji da karuwar farinciki ta hanyar sauraron muryarki, tabbas rayuwarki mai tsarice. Duk wani abu dazan furta agareki bai wuce ince ina sonki va.
 13. Kece tauraruwar dake haskaka zuciyata. Sannan kina ɗaya daga cikin mutanan da baxan taɓa mantawa dasu arayuwata ba haƙiƙa sonki da ƙaunarki baqaramin kamu yayi a birnin zuciyata ba. 
 14. Kece hasken ranar dake haskaka min dare domin nasan safiya ta yi acikin duniyata, ke ce iskar da nake shaƙa domin na rayu, ke tamkar igiyar ruwa ce a cikin kogin da nake ninƙaya kullum safiya, kece bugun zuciyata da yake bambance rayuwa da mutuwata ga ruhina.
 15. Son da nake miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata. Koda a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa zaki tarar dake a cikin shi. Son ki ya zamo jini a jikina yabi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata. 
 16. Ranar da za'a ce gaki a kusa dani, a wannan ranar zan jini a matsayin cikakken mutum mai sa’ar da babu irin sa, a wannar rana zan yi takun ƙasaita tamkar na sarkin da ke da daular da babu irin ta a duniya, saboda na mallaki mai kyawun da babu kamar ta, wadda nake fatan mu rayu tare rayuwa ta har abada.
 17. Ina hango mana rayuwa mai tsawo cike da farin ciki cikin shekaru masu ɗauke da ranaku masu ban mamaki a nan gaba insha Allahu.
 18. A dukkan lokacin da tinanin kyakkyawar fuskarki ya bijiro a cikin zuciyata, sai na ji zuciyata ta ƙara narkewa a cikin soyayyarki, na ji na kamu da matsanancin begen ki, kewarki maras misaltuwa ta dabaibaye ni ta yadda nake kasa tsaida zuciyata daga tinaninki.
 19. A lokacin da taurari suka kasance suna haske saman duniya da haskensu, mu kuma mu kasance tare a ƙasanta muna masu haske cikinta, wannan abu ne da zuciyata tini ta aminta da shi tare da ƙaguwa wajen ganin mun kasance tare tamkar jini da tsoka, zan so a kullum ke ma kamar ni burin son ganin faruwar hakan ya kasance a cikin zuciyarki.
 20. Macen da murmushinta ke haska duhun dare, macen da sautin muryarta ke sanya nutsuwa a zuciyar mai sauraro. Kin samar da farin-ciki a cikin zuciyata, kin zamo mace ɗaya tilo da babu kamar ta a cikin idanuwana.
 21. Jarumtakar Gwanintar Zama Gwani Sun Samu Matsuguni Ga Duk Mutumin Daya Samu Nasarar Zama Jarumi A Gabanki
 22. Nazo Gareki Da Bukatuwar Samun Goyon Baya Da Hadinkai Domin Samun Damar Tayaki Nishaɗi Akowace Rana
 23. Tsirarrun Baituka Na Musamman Na Yabon Sarauniya Ta Musamman Wadda Girman Sarautarta Ya Mamaye Duniyar Masoyan Asali
 24. Matsakaiciyar Kyan Zubin Halittarki Tayi Nisan Awon Gaba Wajen Shantaƙewa Dani Cikin Dausayin Ni'imar Tunaninki.
 25. Bazan Sassauta Akan ƙaunar Abinda Nake ƙauna Ba Dan Haka Karki Sassautawa Zuciyata Wajen Saƙar Mata Lallausan Murmushinki.
 26. Farkawar Baccina Cikin Lokaci da Kammaluwar Mafarkinki Ya Bayyana Saina Tashi Da Zumuɗin Murnar Samun Kallon Kyawun Fuskarki
 27. Aminci Agareki Ya Abun Kaunar Ruhin Jikina, Farin Cikin Dake Wakana Acikin Raina Shine Samun Labarin Kina Cikin ƙoshin Lafiya
 28. Alaƙantuwarmu Da Juna Ce Tasa Na Dauwamar Da Kalmomin Rubutuna Kacokan Dominki 
 29. Zuciyata Tana Mararin Kallon Fuskarki Adaidai Lokacin da Zumuɗin Son Haɗuwata Dake Ya Bayyana
 30. Alhamdulillah Nagode Allah Dayaban Masoyiya Irinki Mai Farin Cikin Ganin Farin Ciki Atare Dani
 31. Sarautar Da Harshe Yake Jagoranta Wajen Isar Da Jagorancin La66an Baki Da Haƙora Cikin Hikimar Sarrafa Zance Mai Bubbugowa Daga Karƙashin Umurnin Zuciyar Mamalakinta
 32. Sun Samu Isar Cika Wajen Jiran Umurnin So Wanda Zai Mallaki Jijiyar Data Kewaye Zuciyar Dake Yawan Tunaki Akowace Rana
 33. Dan Karamin Sakone Mai Cike Da Hikimomin Alƙawuran Dana Sadaukar Da Rayuwata Musamman Wajen Ganin Tabbatuwar Hakan Ta Tabbata
 34. Ladabin Zance Masarrafin Jinin Cikin Ruhi Ya Wadatar Da Rai Wajen Himmatuwar Ganin Zuwan Sakon Murmushi Yana Fitowa Daga Fuskarki
 35. Sallama Daga Fadar So Zuwaga Sarauniya Mai Mulkin Gidajen ƙauna Wadda Tasamu Kafuwar Daula Cikin Mashahurin Birnin Rayuwar Ruhin Jikina
 36. Inason In Sake Jaddada So Zuwaga Wadda Nakeso Domin Nakara Samun So Akan Abinda Nakeso
 37. Wani Lokaci Cikin Wata Rana Na Kasantu Da Shauki Marar Shamakin Abinda Raina Yake Yawan Kallo Kyakkyawar Fuska Wadda Tasha Ado Da Murmushin Alfarma
 38. Kin Iya Tsara Kwalliya Mai Abun Burgewa Hannayenki Basa Rabuwa Da Zanen Lalle
 39. Matattarar Jini Acikin Hanta Sun Koyi Darasin Zama Da Juna Ne Daga Garemu Tayanda Muka Himmatu Wajen Kulawa Da Bagaren Junanmu
 40. Masoyiyata ko kin san cewa cikin kowace rana kyawunki daɗuwa yake yi a cikin idanuwana? Tabbas ba zan dakata daga begen kallon kyakkyawar surarki a zahiri da kuma cikin zuciyata ba har sai gobe hasken idaniyata, hmm! karda ki manta a goben ma sai gobe. Ina son ki.
 41. Tabbas Furanni suna da ƙamshi, Zuma kuma tana da zaƙi launin ciyawa kuma kore ne, amma ke babu wata kalma da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai na ce ke kyakkyawa ce. Ina son ki.
 42. So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take ɗauke a jikin gangar jiki ma’abociyar zuciyar da take ƙunshe da So. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato baƙin-ciki da kuma farin-ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi.

Post a Comment

Previous Post Next Post