GOODNIGHT LOVE TEXT MESSAGE (KALAMAN SOYAYYA NA SAIDA SAFIYA)

 GOODNIGHT LOVE TEXT MESSAGES


Kamar Yadda Muka yi muku bayani cewa shi soyayya yana buƙatar banruwa koda yaushe, mun kawo muku wasu kalamai masu ɗaukar hankali sosai kuma zaku iya amfani dasu wajen turawa masoyan ku.

1. Abu ne mai sauki naso ki, amma abu ne mai wuya na iya rabuwa dake. Naso ace kina tare dani cikin daren nan, yayin da zamu sha hira mai dadi, bana iya cireki cikin tinani na, duk da haka kina cikin zuciyata.

2. Nayi miki Alƙawari zan faɗa miki gaskiya bazan miki ƙarya ba, kuma zan fahimce ki acikin duk wani abu da kikai min. Ina mai tabbatar miki cewa zan kasance mai gaskata ki.

3. Fiye da Sauran Taurari Kike A wurina, Ina Qaunarki ako wani mafi QanQantar lokaci na rayuwata, Rayuwata Soyayyar kice, Soyayyar ki tana Qara Girma acikin Zuciyata ako wani Fita Ta Numfashina. Bazaki taba min laifi ba.

4. So Wani abu ne da ba wanda zai kishi; wani irin yanayi ne da muke gani atare da masoyan mu; yana iya faruwa ako wani lokaci, cikin sauri ko rashin sa; Maganin damuwa ne ba tare da yayi Esfiya ba.

5. Wani mutum, a wani wuri, yana ta mafarkin Murmushin ki tare da Girmama kasancewarki a raye. So duk lokacin da kike cikin Baƙin ciki, ki sani cewa wani mutum, a wani wuri, yana nan cikin kogin tinanin ki.

6. Dearest, I just want to take a moment to tell you how much I adore you on your birthday. Zanyi komai domin na saki farin ciki a wannar ranar. Kin cancanci Ƙaunar da nake mikj, domin kin zama sweetest, kindest, and most caring partner da ɗa namiji zai so samu. Ina Fatan a sauran rayuwarmu, we will be able to celebrate your birthday with you every year. 


7. Sweetheart, Idan na kalleki, sai na gane lokaci yana wucewa, Soyayya ta agareki yana girma sosai, kuma burikan mu yana cika a hankali. Kece ta farkon sanar da duk wani abu daya samen na farin ciki. Na yarda dake kuma nasan zaki sharemin hawayena, nasan zaki rarrasheni idan wani abu ya faru dani maras daɗi.


8. Nine Mafi dacewa dake Sahibata, saboda ina da BestyNa a kusa dani. Babu wata mace da zata iya Jayayya dake, ki sani ni masoyin kine. from the one who adores you.


9. Kasancewa ba'a kusa dake ba Akwai daci tarw da wuya mai tsanani. Duk inda na kalla saina tina dake, sai nace inama dare baya rabamu. Rashin ganin ki gizo yake min HubbyNa.


10. Idan muka bata tsawon lokaci tare Ina jin shauƙi. Hakan baya sakawa nace bana tinanin ki idan bama tare. Yanxu ma ji nake kamar kina gefe yayin da nikuma nake rubuta miki wasiƙar nan. Kin saka hannun ki akan kafaɗuna, Yatsun ki Bisa Kaina. Darling, I adore you.


11. Bugun Zuciyarki ce ke tada numfashina yayin da na nemi kaina na rasa acikin birnin zuciyarki. Yayin da bana iya gane kaina, kece Madubina. Duniya akwai daɗi idan na kalli cikin idanun ki. Ina Girmama adon ki da kwalliyar ki. Kina da jan hankali bansan ko kin san haka ba. Ina tare dake koda zasu ƙiki.


12. A saman Komai, ina godiya da kika kasance ni. Kece ruhin da na jima ina mafarkin samu. Kina tunzura Soyayyar dake zuciyata zuwa Gareki. Nayi shiri tsaf domin tinkarar ki ako wani lokaci acikin ko wani yanayi. Kece madubi na.


Goodnight love text message
13. Ba sai kin tambayi yaya adadin ƙaunar da nake miki ba. Kece Hasken Rana dake haskaka samaniyata, Kogin dake gudana acikin zuciyata, dakuma iskar da nake shaƙa. Bana tinanin yin Soyayya da wata da gaske har sai dana haɗu dake. Amma tunda na haɗa tafiya dake, kin bani yarda da aminci har sai dana gane Soyayyar gaskiya na raye.


14. Kowane lokacina tare dake ina samun farin ciki maras iyaka. An Halicci Hauwa'u daga haƙarƙarin Adamu, wannan kalmar na jita a jikina, domin ke wata bangare ce a jikina. Ina matuƙar farin ciki da godiya da kika kasance wata bangare na rayuwata.


15. Da ace akwai wata hanya ta tabbatar da irin son da nake miki, da nafi kowa iya zayyanawa. kamar kowane lokaci, gwagwarmaya da gogewar rayuwata sun fara haɓaka ne daga lokacin da na haɗu da ke. Kece Shalelen zuciyata.


 16. Duk lokacin da na tuna da ke ko nake tare dake, shi ne babban abin jin daɗi na. Kece farin cikin rayuwata da hasken rana ta. Ni naki ne gaba ɗaya.

 

17. Kin ba ni dukan farin ciki da ƙauna da na nema a duniya. Lokacin da kika shigo rayuwata, kin canza komai. Zan so ki koyaushe! 

18. 

Yin soyayya da ke shine mafi kyawun shawarar rayuwata, amma ba zabina bane. Na kasa shawo kan fado miki. Murmushin ki, halayenki da kamanninki sun sa ba zan iya yin wani abu dabam ba. Kowace rana, Ina samun kaina cikin ƙaruwar soyayyar ki.. 

19. 

Ina son Ki sosai. Saboda ke, komai ina jin zai yiwu. Kina sa ni ji kamar zan iya yin komai. Idan zan iya lashe soyayyar mace mafi Girma a duniya, To zan iya doke duk wani abokin hamayya. 


20. Kullum ke kawai nake Iya Tinawa, Ba kuwa za'a taɓa samun wata kamarki a raina ba. Saboda ke, ina jin farin ciki sosai a rayuwata. Zuciyata ta cika da tunaninki, ina kirga kowacce dakika har sai na sake ganinki. Ina son Ki!

21

Bana mamakin komai a duniyar na, amma na bada tabbacin cewa Soyayya ta gareki gaskiya ce. Babu wani kokwanto akan Adadin Soyayyar ki araina. Tun ranar dana haɗu dake, naji a raina you belong to me. Ina son ki kome zai faru, kuma na yarda na ƙare rayuwata dake.

22

Bazan taba Yaudarar ki ba ko na cutar dake. Ina sonki Sosai har bana son rasaki. Ke haske ce ga duhu na. Idan babu ke, rayuwata zata kasance cikin duhu. Lallai ni masoyin ki ne. Abunda nafi so shine nayi rayuwa dake. Ina sonki.

23

Ki yarda dani ni dake mu fire tare da fuka-fukan Soyayya. Inason ki huta yayinda kike kwance a ƙirjina cikin salama. Ni dake, ina fatan mu kai ga cin ribar Soyayya. I love you completely and unconditionally. Ina Sonki.

24

Burina na zauna dake a cikin birnin Soyayya mai nisan zango. Koda ina cikin baƙin ciki, kallonki nasa komai ya zama normal. Duk lokacin da nake tare dake nakan ji duk wata matsala tawa tazo ƙarahe.

25

Duk abunda mutane zasu faɗa ko ya faru acikin yini, babu abunda zai ɗaukeki daga ina na ajiyeki acikin zuciyata. Ke tawa ce, kuma zuciyata mallakin ki ce. I just want to stay with you forever and ever. You are my true love.

Post a Comment

Previous Post Next Post