HANYOYIN DA ZAKA DAWO DA SHAUKI CIKIN SOYAYYA

 HANYOYIN DA ZAKA DAWO DA SHAUƘI CIKIN SOYAYYA

Duk Soyayyar da ake yinta babu shauƙin juna to wannar Soyayyar tana fuskantar barazanar tabarbarewa. Daga Namijin har Macen Suna da haƙƙi wajen farfaɗo da shauƙi acikin Soyayyar su.

Babu wata hanya da zata cike gurbin Muhimmancin Shauƙi acikin Soyayya. A ƙashin Gaskiya, Shauƙi wani Ɗanɗano ne mai tsaƙi dake Daɗaɗa daɗin Soyayya. Kowa na son Shauƙi a cikin Soyayya Mace ko Namiji. A Dunƙule, Shauƙi wasu ƙananan ayyuka ne da ake yin su ta wata hanya ta musamman dan farantawa juna. Zan Baku Wasu Shawari Guda 9 da zasu Farfaɗo da Shauƙin juna acikin Soyayyar ku.

1. Yawan kiran Masoyiyar ka acikin Rashin Zato.

 Ɗaya daga cikin dabarun dawo da shauƙi acikin Soyayyar ku shine kana kiran Masoyiyar ka a Lokacin da bata tsammani kawai dan kace mata Ina Sonki, ko Kace Mata Tinanin ki nake, kawai saboda ka inganta Soyayyar ka, ko dan ka sanar da ita cewa kana sonta. Kada kayi ƙasa a guiwa wajen fitar da Tsoro, Girmama Head, Jiji Dakai dan Ka Bayyana mata yadda kake ji. Ko Ki Bayyana na mishi yadda kike ji dashi.

Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWAREWA-SOYAYYA

2. A Samu Flower Mai Kyau A Tura mata Gida

Duk da Rike Fure Ko Flower Ba abune da aka saba dashi ba a wannan Zamanin namu, amma yana da matuƙar muhimmanci, domin mata kullum suna son a rinƙa zuwa musu da abunda basa zato basa tsammani. Dama Soyayya tana tafiya da furenni masu ƙamshi. Mata suna son fure.

3. Tsawaita Runguma (MA'AURATA)

Runguma wani Yare ne na Soyayya da Maza Da Mata Suke Buƙata. Ka Samu lokacin baiwa matar ka Runguma mai mai daɗi, kuma mai tsawo batare da kace mata uffan ba.

Karanta: ABUBUWA-GOMA-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA

4. Kuna Fita Yawon Buɗe Ido (MA'AURATA)

Mata fa ba Ƙajin Bitinare bane da Za'a na ajiyesu a gida Koda yaushe. Su dai ana Kula dasu ne kamar kajin Bitinare amma basu ɗin bane.

Yakamata ana Samun Wani lokaci ko Sau ɗaya ne a cikin Wata ɗaya ana Fita dasu yawon Shaƙatawa ana ɗan shan Ice crewa haka.Karanta: YADDA-AKE-GANE-SOYAYYAR-GASKIYA

6. SAƘONNIN SOYAYYA

Yadda Wasiƙun Soyayya suke taimakawa wajen Gyara Soyayya abun Ba'a cewa komai. Idan kana yawan turawa Masoyiyar ka wasiƙun Soyayya tasirin su baida Farashi, domin anan ne ake baje kolin Soyayyar Zuciya, ake faɗin abunda ake ji a cikin Zuciya na shauƙi. Ka yawanta Turawa Masoyiyar ka Wasiƙun Soyayya Na ɗaya daga cikin Abubuwan dake Sarrafa Soyayya cikin sauƙi.


Karanta: ABUBUWA 5 DAKE SA NAMIJI FARIN JINI A WURIN MATA


7. Kana Taya Matar Ka Girki (MA'AURATA)

Kana Taya Matar ka Girki, Renon Yara, Idan Bata da Lafiya Kai Mata wanki Harma da wanka. Share Share, da dai sauran su. 

Akwai Shauƙi Sosai acikin taya matar ka aikin gidan yana ƙara ƙima dakuma shauƙi na Soyayya, Sannan Zata ƙara sonka saboda kana Tausaya mata.

Karanta: DABARU 15 DA MAZA KE AMFANI DASU


8. KISS

Kiss Yana da ƙarfi sosai wanda shine abu mafi ƙarfi wajen janyo shauƙi acikin Soyayya. Yana saka ƙasusuwan Jikin Masoya Haɗuwa da Juna. Kuma ma'aurata ku yawanta yin kiss domin abune wanda yafi saurin kawo Shauƙi.

Karanta:HALAYEN-MATA-TA-GARI

9. WANKA TARE (MA'AURATA)

Kana da Mata Bakwa Wanka Tare? Baku more ba. Yin wanka tare shawari ne mai ƙarfi ga duk ma'aurata. Idan har zaka kwanta gado ɗaya da matar ka, wani lokacin a manne da juna, to babu abunda zai hanaku wanka tare.

Post a Comment

Previous Post Next Post