ABUBUWAN DAKE LALATA SOYAYYA
Damar da Soyayyar ka take dashi dan yin nasara ko faÉ—uwa ya dangana ne da irin daka Shuka a gonar ka. Mutane suna yawan shigo da abubuwan da basu dace ba acikin Soyayya ba tare da sun yi tinani ba. Akwai wasu Halaye da Za Kuyi acikin Soyayyar ku ko cikin auren ku wanda ke saka Soyayyar ku ta zamo kamar gawa mai tafiya.
Idan har ka karanta waÉ—an nan to ka kauce musu:
1. ÆŠaukar Rashin Fahimta A Matsayi Laifi.
Ya danganci irin matakin da kuke ɗauka yayin da kai da masoyiyarma kuka samu Rashin Fahimtar juna. Idan kuka ɗauki hakan kamar faɗa to babu wanda zai yi nasara sai dai ma kuyi asaran Soyayyar ku wajen ƙarar da shauƙin ku.
Abune wanda yakamata ma'aurata su sani cewa Bako wani faɗa ne idan sunyi sai sun samu nasara ba, yakamata ɗaya ya sakarwa ɗaya saboda a samu zaman lumana da Ƙaunar juna. Kada ƙaramin abu yasa ku saurin fushi, Kafun kayi fushin ka fara binciken taya abun ya faru is better.
2. Cutar Da Junan Ku Acikin Kalaman Ku
Babu daÉ—i idan kayi magana aka mayar maka da irin wacce baku so. Idan za kuyi magana da junan ku, to kada kuyi shi cikin fishi, ko Nuna tsana ko Magana kamar kuna faÉ—a, haka babu Soyayya acikin lamarin. Yana É—aya daga cikin iya zama da masoyi ka koyi controling na Bacin rai, kana nitsuwa tare da Jan dogon numfashi idan an bata maka rai.
Idan har ka kasa haƙuri ka mayar da martani mai zafi za kayi dana sani daga baya, wanda kuma Ba'a son haka na faruwa acikin zamantakewa ta Soyayya kota auratayya. Sannan maganar da kayi me zafin nan zata iya zama silar wargaza yardar dake tsakanin ku harma ita kanta Soyayyar.
3. SON KAI (THINKING ONLY ABOUT YOURSELF)
Ka daina saka kanka a farko aduk lokacin da zakai wani abu acikin zamantakewar aure kota Soyayya. Sannan ka daina fifita kanka akan na masoyin ka. Ka koyi yadda zaka bi da Masoyiyar ka daidai da kanka wajen yi mata adalci. Kadaina saka kanka farko, babu adalci acikin hakan sannan yana cutar da zama na Soyayya kona aure. KARKA TABA YIWA WANI ABUNDA IDAN ANYI MANA BAZAKA JI DAÆŠI BA.
4. WAITING.
Ka daina Jiran Masoyiyar ka ta fara kiran ka lo tura maka saƙo ko yi maka magana. Sannan ka daina jira wai saita baka haƙuri idan kunyi faɗa, lamari na yau da kullum sai ana haɗawa da haƙuri, kaina babba akan ta, dan haka kaine zaka bata hakuri sannan ka rarrashe ta. Soyayya yana da wahala sannan Ba'a saka girman kai. Musamman idan kaina baga da gaskiya. Kada ka bari Alfahari da Jiji da kai ya tarwatsa muku Soyayya.
5. KAMAN TA MASOYIYAR KA DA WATA
Acikin Soyayya Ba'a kamanta masoya da wasu daban, kada ka yabi wata a kusa da Budurwar ka ko saurayin ki, hakan yana janyo Rugujewar Soyayya. Babu wanda zai jo daÉ—i acikin ku idan É—aya ya kamanta É—aya da wani. Idan har ka saba irin wannan to ka daina.
6. CACAR BAKI
Yin Cacar Baki acikin mutane ba ƙaramin Matsala bace domin tana iya haddasa rigima tsakanin Masoya mai tsauri kuma mai girma.
Ku koyi yadda zaku Haɗiye bacin ranku cikin Jama'a sai idan kuna inda bamai Kallon ku sai Allah. Sirri yana matuƙar gyara Zaman Soyayya.
7. DAWO DA ABUNDA YA WUCE
Duk abunda ya wuce a barshi karma a tina shi, duk abunda ya faru to ya faru kada a dawo dashi daga baya. Babu amfanin dawo da barna tunda ba iya gyara shi Za'a yi ba. Hakan kuma zai iya janyi Tsauri da damuwa a tsakanin ku.
Muna godiya da Gudummawar ku. Ku ajiye mana Comment.