HANYOYIN DA ZAKA NUNAWA MACE SOYAYYA
Rashin fahimta yana daga cikin abubuwan dake kawo cikas acikin Soyayya. Mafi yawancin lokuta Gyarashi ba abune mai wahala ba. Kawai yadda zaka gyran ne baka sani ba.
Mata koda yaushe suna son a fahimce su Sosai, sannan a nuna musu Soyayya. Idan kana son mace to kayi amfani da waɗannan hanyoyin ka nuna mata Soyayya.
1. Kana Faɗa Mata Manyan Sirrikan Ka.
Babu wani wahala acikin rarrashin Budurwar da kake so. Zaka iya nuna mata kana sonta ta hanyar bayyana mata wasu sirrika naka komin girman su. Duk wanda yasan wasu sirrikan ka na boye kuma manya to zaka ga yana girmama ka sannan zai zama wani bangare naka. Kawai ka kasance mai baiwa Budurwar ka sirrinka banda ƙarya.
2. Kana Neman Shawarinta
Wannan Zai nuna mata cewa lallai kana mutunta bayan Soyayyar da kake mata. Shawarin kuma kar ya zamo babba, ƙanana Kamar su Wani irin kaya yakamata kana sakawa, wani aski za kayi, wani irin takalmi zaka siya. Irin waɗannan maganganu na neman shawarin mace zasu ingizata zuwa tsakiyar kogin Soyayyar ka.
3. Kuna Tsara Rayuwarku Ta Gaba Tare.
Ka nuna mata cewa kaifa Soyayyar ku ta har abada ce baka fatan ku watse wataran. Kana yin Bajet da ita kuma bayan kayi kana faɗa mata. Kuna tattauna Adadin ƴaƴan da zaku haifa tare. Kana tura mata Message dake nuna mata cewa kana son bayan aure kuna yin kaza da zaka. Misali kaɗan idan kayi da mace yana ƙara ƙarfin Soyayya.
Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE
4. Kana Kallon Cikin Idanun ta.
Kana barin idanun ka suna isar da saƙon Soyayyar ka izuwa idanun abar ƙaunar ka. Karka ji kunyar haɗa idanu da ita domin wannan na tura saƙo mai muhimmanci. Itama da kanta zata ga Soyayya acikin idanun ka yayin da kuka haɗa idanu.
5. Kana Riƙe Hannun ta
Kada kana barinta tana aikata komai kai tsaye batare da kana bata shawarwari ba. Duk abunda za tayi idan ya kauce hanya kayi ƙoƙari wajen dawo da ita kan hanya domin mata sai ana kulawa dasu. Lokacin da kuke Soyayya lokaci ne na gyara, kome kace tayi za tayi nan take matuƙar tana ƙaunar ka Sosai.
Karanta: ILLOLIN CIN NAMA DA YAWA, MUSAMMAM JAN NAMA
6. Kana Girmamata.
Na Ƙarshe, kuma mai muhimmanci, kana Girmama Soyayya ka gareta, ka Girmamata ita kanta. Girmamawa abune da ake so a cikin Soyayya, kuma rashin sa kan saka Soyayya lalacewa acikin ƙanƙanin lokaci.
Sannan kana girmama shawarinta, Ko zabin ta, da kuma iyakokin ta. Hanya mafi girma dakuma dacewa ka nuna mace kana sonta shine ka Girmamata.