HANYOYI 16 DA ZAKA SA BUDURWAR KA KO MATAR KA CIKIN FARIN CIKI
Hanyoyin da zaka bi domin saka burdurwarka ko matarka farin ciki, sannan idan kayi amfani da wannan Shawarin Ba kai babu damuwa aciki Zamantakewar ka da Abokiyar Rayuwar ka.
Idan kaje wajen ta ko ka shiga gidan Su ka ce 'Assalamu'alaikum.
Ka riƙa yawan bata labarai Saboda Allah (S.W.T) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.
Ka zama mai yawan yabon ta musamman a wajen da ake kushe ta ka nuna 6acin ranka.
Ka zama mai yawan bata kyaututtuka domin Kyauta tana kara Danqon soyayya.
Ka share wasu daga cikin kuskurenta Ka nuna baka ma san ta yi ba sannan Kuma ka dauka a matsayin abin ya shude kar ka ajiye shi a kwakwalwar ka.
Ka nuna mata tausayawar ka gare ta a fili musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada, ko Rashin lafiya.
Kada ka daukaka abokan ka fiye da matar ka, (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana'a sama da matansu).
Ka nuna mata babu wata budurwa dake gaban ka sai ita tare da nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurin ka.
Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka Hakan zai kara kauna tsakanin ku.
Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyauta da kake mata kamar siyan abinci Saboda daman hakkin ta ne ka kawo mata, sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.
Karanta: YADDA-AKE-DAINA-ISTIMNAI
Ka dauki abinci ka saka mata a baki Annabi (SAW) Yace "abincin ba cikin ta kadai zai shiga ba zai wuce har zuwa zuciyar ta."
Ka kasance mai yawan yi mata murmushi fara'a domin Manzo (SAW) Yace,"duk wanda ya nunawa matar sa fara'ar sa to dai - dai Yake da yin sadaka."
Ka zama mai yawan neman shawarar ta (wasu suna ce wa ba'a shawara da mata) To ku sani cewa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matan sa.
Karka 6oye mata damuwar ka farin cikin ka ko bakin cikin ka, Domin ita magani ce a tattare da kai.
Kada kayi mata fada alokacin da tayi maka laifi, kabari sai kun samu nutsuwa.
YADDA ZAKA SACE ZUCIYAR MACE DA SOYAYYA HADUWAR FARKO
Mata Wasu Nau'in Halittune Wanda Allah ya halitta domin mu maza. Ba ko wani namiji bane zai iya rayuwa ba tare da mace ba, haka bako wace mace bace zata iya rayuwa babu namiji ba. mata wasu halitta ne masu ban mamaki da ƙawa ga kyawun Halitta haɗi da burgewa.
Babu namijin da zai ƙyalla idanu ya hango wata Kyakkyawar mace, batare da ya ji wani abu a cikin ranshi ya motsa ba.
Mata suna da abunda suke so game da maza kamar yadda maza ke da abun da suke so a game da mata na daga cikin nau'in hallita ko Halayya. Wannan abubuwa suna da yawa, wasu daga ciki sune, Kyawun Fuska, Kyawun Jiki, yanga, zaƙin murya, iya tafiya wannan a Bayyane kenan, amma a boye ko wani namiji da kalar macen da yake so, kuma yake Ƙauna.
Me zai faru idan ka ƙyalla idanu ka hango mace a kusa dakai, kuma Kanason mata magana?
Ga Wasu Sabbin Hanyoyin Da Zakabi.
1. Ka Tabbatar Ka yi Shiga me kyau sosai. irin adon da kai kanka kasan ka fito gari, Kuma kayiwa kanka kyau, domin su mata Allah ya yi su da son ado da kwalliya. Idan kana da gemu ka gyara shi.
2. Sai Kayi Duba Zuwa ga Ita Budurwar, Wani Irin Shiga Tayi? Domin Yanayin Shigarta Yanayin Kalaman Da Take Buƙata, Kasan Mata akwai girman kai Musamman Idan sun ci ado suna taku ɗai-ɗai Bisa hanya.
3. Bayan ka Karanci Yanayin shigar da tayi da tafiyar ta, sai ka tunkari inda take, karka iso kusa da ita a dai-dai lokacin da kuke kusa da taron jama'a domin su mata akwai kunya musamman cikin Mutane, kai kasan irin kalaman da zaka yi mata domin kaine ka dube ta da kyau. ka turomin hoton ta saina duba maka amma idan tana DA kyau.
4. Karka ce mata Ƴan mata, karka ce mata ƙanwata. Kace Mata Baiwar Allah, yayata ko ƴar uwata. Me matsayi ce ko talaka ce, Domin baka san yanayin girman kanta ba, tana da shi ko batada girman kai. Kana dan Murmushi, da motsa jiki na Yanga Amma Irin Yangar mu ta Maza fa tam.
5. Idan tafiya take, to lallai akwai inda zata, Gida ta nufa ko unguwa, biki ko makaranta. To kai mata uzuri a cikin kalaman ka wajen tsagaita su.
6. Karki ce na saka miki ido, Amma Tun daga can nake biye dake, Naga Kamar Zaki Anguwa ne banson na tsayar dake.
7. Zaka Iya Fara mata da Gaisuwa, Mata suna son a Girmama su sosai. Kasan su akwai Son Mulki da Gadara da IZZA.
Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA
8. Kada na Tsaidaki da yawa, inason kiban dama na FaÉ—a miki wasu Tsaftatattun Maganganu Amma Ba Anan Ba, A wani wuri mai Kyau mai Tsafta. Domin Na Alkhairi ne.
9. Wasu matan sukan danyi magiya sosai kafun a shawo kansu, Sai ka Iya Bakinka wurin Tsara su, Ka Tabbata ta Baka number waya kuma ka kira a lokacin ya shiga. Wasu suna bata Wrong number idan bakai Good Performance ba a kula.
10. Ka Tabbatar ta FaÉ—a maka lokacin da zaka Kirata, Da Yammaci ko da dare. Kada kayi latti wajen kira kuma ka Tabbatar ka samu wuri wanda ba mutane sosai. Domin ka samu damar Zazzago kalaman da suka Dace.
Gargadi: A wannan zamani mata basa amincewa da yaudara, duk macen data samu saurayi ba abun da take so take ji a bakin shi kamar taji maganan aure, acikin kalamai na yau da Kullum.
Satin farko dolene ka sace mata zuciya da Kalamai wanda zasu hura mata kai, Taji cewa ta fara sabuwar rayuwa.
Ku kasance da Shafin www.Qauna.com.ng Shafin MASOYA ne bana maqiya ba.
Mun Gode.
ABUBUWA GUDA 11 DA ZAKA YI KA SAMU SOYAYYAR MACE
Zan Lissafo Abubuwa guda 10 da ko wace mace take so, amma basa iya tambaya dan ayi musu, amma idan kana yiwa Budurwar ka, zata soka fiye da tsammanin ka.
1. Ka kira ta da Safe, ka tambayeta ya take, sannan ka faÉ—a mata yadda kake son ta, sannan ka mata addu'a mai daÉ—i.
2. Kada ka mata ƙarya: mata basa son namiji wanda yake musu ƙarya. Komai tsakanin ku ka faɗa mata gaskiya. Sannan kasan hanun ka!
3. Kana nunawa abokan ka cewa kana son ta sosai, musamman a idon ta. Kana yabon ta a wurin abokan ka idan tana wurin zata ji daÉ—i.
4. Ka tabbatar duk wata matsala tata Kana ƙoƙari wajen magance mata, koda bakada iko kayi naka ƙoƙarin.
Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-BI-KA-SACE-SOYAYYAR
5. Kana Nuna godiyar ka a fili idan tai maka alheri wato kyauta.
6. Kana Yawa Janyo abunda zai sa kuna jinawa kuna hira, mata suna son ana basu labarin abun dariya.
7. Kana Yawan Bata Kyauta Musamman kayan Kwaɗayi wato Ƙwalama
Karanta: SHAWARI GOMA GA MASOYA
8. Hangout with her and your friends together and hold her hand in public.
9. Ka nuna mata Baka da kowa sai ita, Kana Tina Mata Alkawarin dake tsakanin ku na soyayya da riƙon amana.
10. Kada Kana yawan fishi Idan kuna hira, ko da wasa ne zata É—auka da gaske kake.
11. Ka nuna mata idan tana tare dakai Tana cikin tsaro da kuma gata, komai zaka iya yi mata.
Muna Godiya.
Tags
Love guide